Bukatar Dakatar da Rikicin Gabas ta Tsakiya Kafin Ya Kara Tsananta

[ad_1]

Rahotanni na nuna cewa, bayan wata guda da fara hare-haren hadin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila kan Iran, yankin Gabas ta Tsakiya na kara fadawa cikin rikici mai tsanani, inda yawan mace-macen fararen hula ke karuwa, yayin da rikicin ke kara yaduwa zuwa wasu sassa na yankin.

Bincike ya nuna cewa, wannan rikici bai zama dole ba, domin akwai hanyoyin diflomasiyya da za a iya bi kafin fara hare-haren amma aka yi watsi da su, sabi da rashin girmama tsarin doka na Majalisar Dinkin Duniya, lamarin da ya kara dagula al’amura maimakon kawo mafita.

Masana harkokin kasa da kasa sun bayyana damuwa kan yadda aka kaddamar da wadannan hare-haren na son rai, musamman dangane da rashin samun amincewar Kwamitin Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya kafin daukar matakin soja, wanda hakan na iya kawo cikas ga dokokin kasa da kasa da kuma rage darajar tsarin doka a duniya.

Rahotanni sun nuna cewa, maimakon samun kwanciyar hankali da Amurka ta yi ikirarin samarwa, hare-harenta sun kara jefa yankin cikin wani hali mawuyaci. Tarihi ya nuna cewa, irin wadannan matakan hare-hare na Amurka, ba sa haifar da komai, sai dai haddasa rashin zaman lafiya mai dorewa, kamar yadda aka gani a sauran kasashen da irin hakan ta faru da su, kamar Libya, Iraki, Afghanistan da Syria.

Masana sun jaddada cewa, hanyar soja kadai ba za ta iya kawo cikakken tsaro ba. Sun ce yankin na bukatar zaman lafiya, ci gaba da tattaunawa, da kuma hanyoyin siyasa domin warware matsalolin da ke akwai.

Sam bai dace ba, manyan kasashe su rika take kanana, kamar ana rayuwar dabbobin daji. Ya dace, kasashen duniya su guji daukar matakai na kashin kai, su kuma mutunta dokokin kasa da kasa domin tabbatar da adalci da zaman lafiya a duniya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *