Yunƙurin Tinubu Na Mayar Da Kano Jiha Mai Jam’iyya Ɗaya Zai Ci Tura — Tanko Yakasai

[ad_1]

Wani ɗan siyasa kuma tsohon ɗan takarar Jam’iyyar PRP a zaɓen 2023, Salihu Tanko Yakasai, ya zargi Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da yunƙurin amfani da dabarun siyasa wajen mayar da Jihar Kano jiha mai jam’iyya ɗaya, yana mai cewa wannan tunani kuskure ne mai girma.

Yakasai, wanda shi ne tsohon mai taimaka wa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ɓangaren yaɗa labarai, ya ajiye mukaminsa kwanan nan tare da ficewa daga Jam’iyyar APC, inda ya koma Jam’iyyar ADC, sakamakon rashin gamsuwa da yadda ya ce ake tafiyar da mulki a ƙarƙashin shugabancin Tinubu.

  • Harin Filato: JNI Ta Tabbatar Da Kashe Mambobinta 4, 10 Sun Ɓace
  • Farfadowar Halittun Ruwa A Kogin Yangtze Ta Nuna Kyakkyawan Yanayi

A cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar 1 ga Afrilu, 2026, Yakasai ya ce tarihin siyasar Kano ya nuna cewa tun daga zamanin jam’iyyar Northern Elements Progressive Union (NEPU) har zuwa lokutan “Santsi da Tabo”, jihar ba ta taɓa zama ƙarƙashin jam’iyya ɗaya ba, kuma hakan ba zai sauya ba. Ya ƙara da cewa, “Kano ba Lagos ba ce,” yana mai nuni da bambancin tsarin siyasa tsakanin jihohin biyu.

Ya bayyana cewa siyasar Kano ta ginu ne kan kishin al’umma, gaskiya da tsayawa kan akida, wadda marigayi Aminu Kano ya shimfiɗa. A cewarsa, adawa a Kano ba don adawa kawai ake yi ba, sai don tabbatar da ci gaban al’umma, ingantaccen shugabanci, adalci da riƙon amana.

Yakasai ya kuma nuna damuwa kan abin da ya kira watsi da korafe-korafen al’ummar Kano, musamman dangane da zargin karkatar da muƙaman gwamnati da kuma fifita wasu yankuna a ayyukan ci gaba. Ya ce irin wannan hali ba zai haifar da goyon bayan jama’a ba.

Ya jaddada cewa biyayya ga shugabanci tana samuwa ne ta hanyar adalci da kyautatawa, ba ta hanyar tilastawa ko amfani da dabarun siyasa da yaudara ba.

A ƙarshe, ya ce idan aka ci gaba da abin da ya kira hana Kano haƙƙinta, al’ummar jihar za su mayar da martani ne ta akwatin zaɓe, yana mai cewa wannan ita ce hanya mafi sauƙi kuma mafi dacewa a tsarin dimokuraɗiyya.

Ya rufe da kalmar, “Falle ɗaya ce (F1).”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *