Atiku Ya Yi Wa Kwankwaso Maraba Da Zuwa ADC

[ad_1]

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya marabci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jam’iyyar ADC. Matakin na nuna ƙara ƙarfi ga haɗakar ‘yan adawa gabanin zaɓen 2027.

Atiku ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook ranar Litinin da rana. Ya rubuta cewa haɗuwar masu kishin manufa ɗaya na girgiza iko tare da yi wa Kwankwaso maraba.

  • Atiku Ya Nuna Damuwarsa Kan Kama ‘Yan Adawa, Ya Nemi A Saki El-Rufai
  • Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Ya Yi Rashin Ɗan Tawagar Yaɗa Labaransa

Wannan sanarwa ta biyo bayan murabus ɗin Kwankwaso daga jam’iyyar NNPP ranar 29 ga Maris, 2026. Ya ce ya ɗauki matakin ne domin yin sabon tsari da ya dace da yanayin siyasar ƙasar.

Kwankwaso ya gode wa NNPP kan damar da ta ba shi a matsayinsa na jagora da ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023. Ya jaddada buƙatar komawa wata jam’iyya da za ta kawo sauyi mai ma’ana.

Hakan ya zo ne bayan wata ganawa mai muhimmanci da ya yi da Atiku a Abuja ranar Lahadi. Dukkaninsu sun bayyana tattaunawar a matsayin mai amfani kan makomar ƙasa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *