HOTUNA: Kwankwaso ya koma ADC

[ad_1]



Tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya koma jam’iyyar haɗaka ta ADC tare da magoya bayansa bayan ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.

An gudanar da bikin komawarsa ne a gidansa da ke Miller Road a unguwar Bompai da ke Kano, inda shugabannin jam’iyyar da ɗimbin magoya bayansa suka halarta domin tarbar sa.

Tsohon gwamnan ya kuma buƙaci magoya bayansa su yi rajistar jamʼiyyar, tare da samun katin zaɓe na ƙasa.

A wannan Litinin ɗin ce dai manyan shugabannin jam’iyyar ADC suka dira a Kano, gabanin sauya sheƙa Kwankwaso zuwa jam’iyyar.

Tawagar, wadda ta ƙunshi fitattun ‘yan siyasa, ta sauka a filin jiragen sama na Malam Aminu Kano, inda tsohon mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya tarbe su.

Daga cikin manyan jagororin da suka sauka a birnin na Dabo akwai tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma shugaban ADC na ƙasa, David Mark; sakataren jam’iyyar na ƙasa, Peter Obi; da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola.

Sauran sun haɗa da tsohon gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; Sanata Dino Melaye; tsohon shugaban APC na ƙasa, John Odigie-Oyegun; da tsohon gwamnan Imo, Emeka Ihedioha.

Aminiya ta ruwaito cewa, kai tsaye tawagar ta wuce gidan Kwankwaso da ke Miller Road a unguwar Bompai, inda ake ci gaba da shirye-shiryen ƙarshe na sanar da sauya sheƙarsa zuwa ADC a hukumance.

Shigowar Kwankwaso ta buɗe sabon babi a dimokuraɗiyyar Najeriya — Mark

Shugaban ADC na ƙasa, David Mark, ya bayyana sauya sheƙar a matsayin wani muhimmin mataki wajen ƙarfafa haɗin kan ‘yan adawa a Najeriya.

“Wannan rana alama ce ta sabon babi a dimokuraɗiyyar ƙasar nan, da kuma yunƙurin gina Najeriya mafi inganci da haɗin kai,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa shigowar Kwankwaso ba wai alama kawai ba ce, illa wani mataki ne na haɗa kan shugabannin da ke da buri iri ɗaya domin samar wa ‘yan Najeriya sauyin shugabanci mai nagarta.

A jiya Lahadi ce dai Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga NNPP, yana mai cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin haɗa kai da wasu jam’iyyu domin kawo sauyi a ƙasar.

Ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a samar da haɗin gwiwa tsakanin manyan ‘yan adawa, domin tunkarar ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta da kuma inganta shugabanci.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *