HOTUNA: Yadda Gwamnan Gombe ya halarci jana’izar mahaifiyar El-Rufai




Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya halarci jana’izar Hajiya Umma El-Rufai, mahaifiyar Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a Masallacin Ƙasa da ke Abuja.

A saƙon ta’aziyya da ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Isma’ila Uba Misilli, gwamnan, ya bayyana cewa rasuwar a matsayin babban rashi.

Ya ce marigayiyar ta kasance mai kirki, mai tausayi da kuma kyawawan halaye, wadda ta yi wa ’ya’yanta tarbiyya mai kyau.

Gwamnan ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga El-Rufai da iyalansa, tare da roƙon Allah Ya ba su haƙuri da juriya.

Haka kuma ya roƙi Allah Ya gafarta mata, Ya karɓi ayyukanta na alheri, Ya kuma sanya ta a Aljannatul Firdausi.

An yi jana’izar marigayiyar ne a Abuja bisa tsarin addinin Musulunci.

Ga hotunan jana’izar:




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *