Mahaifiyar El-Rufai, Hajiya Umma ta rasu
Hajiya Umma El-Rufai, mahaifiyar Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ta riga mu gidan gaskiya.
Ɗan tsohon gwamnan, Bello El-Rufai ne, ya sanar da rasuwar kakar tasa a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a.
“Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un. Daga Allah muka fito kuma gare Shi za mu koma. Ina sanar da jama’a rasuwar kakata, Hajiya Umma El-Rufai, wadda ta riga mu gidan gaskiya sa’o’i kaɗan da suka gabata,” in ji shi.
Bello, ya gode wa Allah kan tsawon rayuwar da ta yi mai cike da albarka. Y
a kuma roƙi Allah Ya jiƙan ta da rahama, tare da neman al’umma su nema mata rahamar Ubangiji.
Ya ƙara da cewa: “Mun gode wa Allah kan rayuwar da ta yi, muna roƙon Allah Ya jiƙan ta da rahama… A madadin iyalinmu, muna neman addu’o’inku.”
Wannan rashi ya zo ne a daidai lokacin da El-Rufai ke fuskantar shari’a, biyo bayan kama shi da aka yi tare da gurfanar da shi a gaban kotu kan wasu zarge-zarge.
Wannan yanayi ya janyo shakku da tattaunawa kan ko tsohon gwamnan zai samu damar halartar jana’izar mahaifiyar tasa.