Sin Da Najeriya Sun Sanya Hannu Kan Shirin Yarjejeniyar Raya Dangantakar Abokantaka A Fannin Tattalin Arziki

[ad_1]

Ministan kasuwanci na kasar Sin, Wang Wentao, da ministar masana’antu, ciniki da zuba jari ta Najeriya, Jumoke Oduwole, sun sanya hannu kan Shirin Yarjejeniyar Raya Dangantakar Abokantaka a Fannin Tattalin Arziki a Tsakanin Gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin da Gwamnatin Tarayyar Najeriya. An rattaba hannun ne jiya Alhamis, yayin taron ministoci na 14 na Hukumar Cinikayya ta Duniya (WTO), kuma wannan shi ne shirin yarjejeniya da Sin ta cimma tare da kasa ta 34 a nahiyar Afirka.

Bisa shirin yarjejeniyar, bangarorin biyu za su hada kai don inganta bunkasar masana’antun kere-kere da yin gyare-gyare a fannin aikin gona a Najeriya, domin kara karfin takarar kasar a kasuwannin duniya da taimaka mata shiga cikin tsarin tattalin arzikin duniya yadda ya kamata. Haka kuma, za su gudanar da shawarwari a wasu fannonin da suka shafi samar da sauki ta fuskar cinikayyar kayayyaki da ta hidima, da karfafa hadin gwiwa kan samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma zuba jari da cinikin dijital da dai sauransu. (Bilkisu Xin)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *