Indomie Ta Gwangwaje Mutane 80 Da Kyautar PS5, iPhone, TV, Firinji Da Kekuna A Gasar Garabasar Samun Nasara

[ad_1]

Kamfanin taliyar Indomie na ci gaba da faranta ran kwastomominsa ta hanyar shirin sa na Garabasar Samun Nasara (Indomie Success Promo), wani shiri ne na musamman da aka ƙirƙiro domin karrama kwastomomi masu daraja tare da samar da kyautuka da za su ke tunawa da su da sanya su farin ciki.

Shiga cikin gasar abu ne mai sauƙi. Ana buƙatar masu sha’awa da su tattara faketin ledojin Indomie guda 10 na sabon fakiti su kai su cibiyar da ake karɓa mafi kusa da su domin samun fakitin Indomie gram 70 kyauta.

  • Bankin Duniya ya Jinjina Wa Jihar Gombe Kan Magance Zaizayar Kasa
  • Yadda Takarar Obi Ta Zama Kamar Wani Wasan Barkwanci

Duk faketin ledoji 10 ana ƙirga su a matsayin maki ɗaya. Yawan ledojin Indomie da ka tattara na ƙara yawan makinka a gasar, ka ci Indomie da yawa, ka ci nasarar lashe gasar da yawa! A ƙarshen kowane wata, mutane 80 da ke kan jadawalin da suka yi nasara da maki mai rinjaye za su samu kyaututtuka masu kayatarwa. Haka kuma, ana iya bibiyar shafin Indomie.ng/arewa, domin samun karin bayani kan gasar.

A wani ɓangare na gasar, Indomie ta shirya wani gagarumin taron Kasuwannin Kano da Kaduna, inda aka nishaɗantar da jama’a. Taron ya tara jama’a da ‘yan-kasuwa masu da masu sayayya inda aka nishadantu da wasanni masu kayatarwa tare da ƙarin rabon kayatattun kyautuka daga Indomie.

Babban abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne rabon kyaututtuka kai tsaye ga wadanda suka lashe gasar, inda waɗanda suka yi nasara suka samu kyaututtuka kamar PS5 da wayoyin iPhone da firiza da mazubin gas na girki da talabijin da kuma kekuna. Wannan rabon kyaututtuka ya sanya farin ciki a zukatan mahalarta taron, tare da ƙara tabbatar da gaskiya da sahihancin gasar.

Da yake jawabi a wajen taron, Jamiu Abdulrasheed ya bayyana cewa: “Ganin farin ciki da annashuwa a fuskar kwastomominmu yana nuna mana cewa duk ƙoƙarin da muka yi wajen shirya wannan gasar ya yi tasiri. Wannan shiri hanya ce ta nuna musu godiya tare da ba su damar cin manyan kyaututtuka.”

Wasu daga cikin waɗanda suka yi nasara sun bayyana cewa nasarar ta zo musu a bazata kuma ta sanya su farin ciki matuka, tare da ƙarfafa wa sauran jama’a gwiwa da su shiga cikin gasar a dama da su suma su amfana.

Baya ga nishaɗi, taron ya taimaka wajen bunƙasa hada-hada Kasuwannin biyu, inda yawan jama’a ya ƙaru tare da hada-hadar harkokin kasuwanci a yankunan da aka gudanar da gasar.

Har yanzu akwai sauran kyaututtuka da za a ci, Indomie na ƙarfafa wa jama’a gwiwa da su ci gaba da shiga gasar tare da cin Indomie domin ƙara samun damar cin nasara a gasar.

Domin ƙarin bayani, ana shawartar jama’a da su rika bibiyar shafukan sada-zumunta na kamfanin musamman @Indomie Arewa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *