Mataimakin Shugaba Sin Ya Gana Da Shugaban Afrika Ta Kudu Kan Dangantakar Kasashen Biyu
[ad_1]
Mataimakin shugaban Sin Han Zheng, ya gana da shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, jiya Alhamis a birnin Cape Town, inda suka lashi takobin zurfafa hulda da dangantakar kasashensu.
A cewar Han Zheng, Sin na daukar dangantakarta da Afrika ta Kudu da muhimmanci, kuma ta shirya hada hannu da ita wajen bunkasa dangantakarsu bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a sabon zamani, bisa matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma.
Ya kara da cewa, taron majalisun dokokin Sin biyu da aka kammala a baya-bayan nan, ya yi nazari tare da amincewa da shirin raya kasar na shekaru biyar-biyar, daga 2026 zuwa 2030. Kuma cikin shekaru 5 masu zuwa, Sin za ta fadada bude kofarta ga kasashen waje. Lamarin da zai samar da karin damarmaki ga hadin gwiwarta da Afrika ta Kudu.
A baya bayan nan, shugaba Xi Jinping na Sin ya sanar da cewa daga ranar 1 ga watan Mayu, ƙasar Sin za ta fara aiwatar da matakin soke haraji baki ɗaya ga kasashen Afrika 53 waɗanda ke da hulɗar diplomasiyya da ita. Game da hakan, Han Zheng ya ce Sin ta shirya hada hannu da Afrika ta kudu wajen kammala tsare-tsaren soke harajin kayayyaki, karkashin yarjejeniyarsu ta hadin gwiwar tattalin arziki domin ci gaba na bai daya, da nufin tabbatar da Afrika ta Kudu ta ci gajiyar matakan soke harajin cikin lokaci mai tsawo ba tare da tangarda ba. (Mai Fassara: Fa’iza Mustapha)
[ad_2]
Source link