Sheikh Abduljabbar ya nemi taimakon alƙalin alƙalai kan zargin yi wa shari’arsa maƙarƙashiya
[ad_1]
Fitaccen malamin addinin nan na Jihar Kano, Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara, ya aike da takardar koke ga Babban Alƙalin Alƙalai na Ƙasa (CJN), inda yake zargin kotuna da wasu jami’an gwamnati da hannu wajen hana shi damar ɗaukaka ƙara kan hukuncin kisan da aka yanke masa.
A cikin wata takarda mai shafuka 14 da aka gabatar wa Kotun Ƙoli a ranar 26 ga watan Maris, Abduljabbar, ya bayyana cewa an gudanar da shari’arsa cikin rashin adalci.
Ya ƙara da cewa akwai maƙarƙashiyar siyasa da aka ƙulla da nufin toshe duk wata ƙofa da zai bi domin samun haƙƙinsa.
Malamin ya yi zargin cewa wasu manyan mutane a Najeriya da wasu daga ƙasashen waje, sun yi ƙoƙarin mayar da shi wani babban jagoran addini kamar Ayatollah Khomeini, amma ya ƙi amincewa da hakan, yana mai cewa yin hakan na iya jefa shi cikin garari.
Idan za a iya tunawa, a watan Disamban 2022 ne, wata Kotun Musulunci a Kano ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan an same shi da laifin yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Wannan hukunci ya haifar da cece-ku-ce da muhawara mai zafi a faɗin Jihar Kano.
A halin yanzu dai, malamin yana tsare a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja.
A cikin takardar tasa, Abduljabbar ya bayyana cewa ya shigar da ƙarar neman ɗaukaka hukuncin tun a watan Disamban 2022, sannan ya sake gabatar da wasu buƙatun a shekarar 2024, sai dai ya yi zargin cewa kotuna na jan ƙafa, ko ma sun ɓata muhimman takardunsa.
Haka kuma, ya zargi alƙalan kotun ɗaukaka ƙara da sauya kwanakin da ke jikin takardun da kuma sauya bayanansa domin biyan buƙatar gwamnati.
Sheikh Abduljabbar ya nanata cewa ƙin yardar da ya yi na zama jagoran juyin juya hali ne, ya janyo masa matsin lamba daga shugabannin siyasa da na addini.
Ya kuma yi zargin cewa akwai sa hannun ƙasashen waje, inda ya bayyana cewa ya taɓa ganawa da wakilan ƙasar Iran da wasu jami’an Najeriya waɗanda suka buƙaci ya shiga wani tsari nasu.
Ya ce har ma an yi masa tayin maƙudan kuɗaɗe da kwangiloli da darajarsu ta kai Naira miliyan 500, amma bai karɓa ba.
Bugu da ƙari, malamin ya zargi tsohon Ministan Ilimi, Adamu Adamu, da hannu a cikin matsalolin da yake fuskanta, ciki har da tura jami’an tsaro zuwa gidansa da masallacinsa.
Ya kuma bayyana cewa akwai haɗin baki tsakanin lauyoyin gwamnati da alƙalai wajen yin katsalandan a shari’arsa, wadda a cewarsa ta saɓa wa sashe na 38(1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da ya bai wa kowane ɗan ƙasa ’yancin yin tunani da bin addinin da yake so.
Har ila yau, ya yi zargin cewa an taɓa yaudararsa aka ba shi wani “ruwa da aka gauraya da wani abu,” wanda ya ce yana da alaƙa da wani shiri na sarrafa tunaninsa.
Ya ƙara da cewa bayan ya ƙi amincewa da buƙatunsu, tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kwatanta shi da Maitatsine, wanda ya taɓa tayar da rikici a shekarun 1980.
A ƙarshe, Sheikh Abduljabbar ya roƙi Babban Alƙalin Alƙalai na Ƙasa da ya gaggauta shiga cikin lamarin, yana mai jaddada cewa shi ɗan ƙasa ne mai kishin ƙasa da aka tsare na tsawon shekaru biyar ba tare da aikata wani laifi ba.
Ya bayyana cewa hukuncin da aka yanke masa cike yake da kura-kurai, tare da yin gargaɗin cewa shari’ar tasa babban misali ne na zalunci da rashin adalci.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link