Mutum 3 Sun Rasu, Wasu Sun Tsere Sakamakon Rikici Tsakanin Hausawa Da Fulani A Kebbi

[ad_1]

Wani rikici da ya ɓarke tsakanin Hausawa da Fulani a ƙauyen Alwasa da ke ƙaramar hukumar Argungu a Jihar Kebbi, ya yi sanadin mutuwar mutum uku tare da janyo mutane da dama suka tsere daga gidajensu.

Rikicin ya fara ne bayan saɓani ya ɓarke tsakanin wasu matasa kan tuƙin babur cikin ganganci.

  • Kusan Shugabannin Kamfanoni 100 Ne Suka Taru Domin Halartar Dandalin Bunkasa Kasar Sin
  • Griezmann Zai Bar Athletico Madrid A Karshen Kakar Wasa Ta Bana

Lamarin ya ƙara tsananta ne bayan wani matashi Bafullatani ya caka wa matashin Bahaushe wuƙa.

Shugaban ƙaramar hukumar Argungu, Sani Gulma, ya ce bayan wanda ake zargi ya tsere, wasu matasan Hausawa sun kai hari ramuwar gayya a wani wajen zaman Fulani, inda aka kashe wasu biyu, kuma mutane da dama suka tsere.

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya ziyarci yankin, inda ya yi Allah-wadai da rikicin tare da gargaɗin a guji ɗaukar fansa.

Ya ce ya umarci jami’an tsaro su kamo wanda ya jawo rikicin domin a hukunta shi.

Haka kuma ya tunatar da al’ummomin biyu yadda suka daɗe suna zaune lafiya tare, tare da yin kira gare su da su ci gaba da zama lafiya.

Gwamnan ya kuma bayar da tallafin Naira miliyan biyu ga iyalan dukkanin waɗanda suka mutu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *