Manufar Kasar Sin Daya Tak A Duniya Ita Ce Tushen Siyasa Ta Shigar Taiwan Ayyukan WTO
[ad_1]
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce manufar kasar Sin daya tak a duniya, ita ce tushen siyasa ta shigar yankin Taiwan ayyukan kungiyar cinikayya ta duniya ko WTO.
Lin Jian, wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, yayin taron manema labarai na yau da kullum da aka saba gudanarwa, lokacin da aka yi masa tambaya dangane da shawarar da mahukuntan jam’iyyar DPP suka yanke, na kauracewa taron manyan jami’an WTO da zai gudana a Kamaru, bayan da aka ambaci Taiwan a matsayin lardi a kasar Sin cikin takardun Bizar halartar taron.
Lin, ya ce kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma Taiwan yanki ne na Sin wanda ba za a taba iya balle shi ba. Kazalika, Sin ta wanzar da matsayarta a fili dangane da batun shigar yankin Taiwan cikin harkokin kasa da kasa. Kuma wajibi ne a warware batun karkashin tanadin manufar ta kasar Sin daya tak a duniya.
Bugu da kari, Lin ya ce tsarin odar cinikayya na kasa da kasa na fuskantar kalubale mai tsanani, kuma salon daukar matakan kashin kai, da kariyar cinikayya na karuwa, yayin da tsarin cinikayya na mabambantan sassa ya ci karo da tarin matsaloli.
Daga nan sai jami’in ya ce abu ne mai matukar muhimmanci, taron ministoci na WTO ya koma nahiyar Afirka bayan shekaru 10, kuma kasar Sin na matukar goyon bayan kasar Kamaru, wajen cimma nasarar taron da za ta karbi bakunci. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link