Shugaban Al’ummar Turkmenistan Ya Ce Idan Sin Ta Yi Kyau Duniya Za Ta Kara Kyau
[ad_1]
Shugaban al’ummar Turkmenistan, kuma shugaban kwamitin jama’ar kasa na Halk Maslahaty na kasar, Gurbanguly Berdimuhamedov, ya ce dangantakar dake tsakanin kasashen Turkmenistan da Sin, ta riga ta kai wani babban matsayi na hadin gwiwa.
Ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin ko CMG a kwanan nan, inda ya ce shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru 34 da kafuwar huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu. Ya kara da cewa dangantakar dake tsakanin kasashen Turkmenistan da Sin na da kyakkyawar makoma a nan gaba.
Hakazalika, ya jinjinawa nasarar da aka cimma yayin manyan taruka biyu na kasar Sin na shekarar nan ta 2026, wato taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa na jama’ar kasar. Kana ya yaba wa shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 15, wanda ya ce zai bude sabon babi na samun ci gaba mai inganci a kasar.
Baya ga haka, shugaba Berdimuhamedov ya bayyana cewa, kasar Sin ginshiki ne na tabbatar da tsaro, da samun dauwamamman ci gaban duniya. Ya ce, “Idan Sin ta yi kyau, duniya za ta kara kyau.” (Mai fassara Bilkisu Xin)
[ad_2]
Source link