Iran ta kai hari sansanin sojin Amurka da Birtaniya a Tsibirin Chagos — Rahoto
[ad_1]
Wani rahoto ya ce Iran ta harba makamai masu linzami zuwa sansanin haɗin gwiwar sojojin Amurka da Birtaniya da ke Diego Garcia a Tsibirin Chagos, cikin Tekun Indiya.
Mujallar Wall Street ce ta rawaito hakan, inda ta ce nisan da ke tsakanin Iran da tsibirin ya kai kimanin mil 2,500, wato kusan kilomita 4,000, lamarin da ke nuna yiwuwar Tehran na da makamai masu tafiyar dogon zango fiye da yadda ake zato a baya.
Rahoton ya ƙara da cewa har zuwa lokacin tattara bayanai, Ma’aikatar Tsaron Amurka Pentagon ba ta yi tsokaci kan lamarin ba.
Sai dai babu cikakken bayani kan irin ɓarnar da harin ya haddasa ko ko an samu asarar rayuka.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link