Sallah: Sanusi II ya buƙaci Musulmi su ɗore kan kyawawan ɗabi’un da suka koya a Ramadan

[ad_1]



Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su ɗore kan kyawawan ɗabi’un da suka koya a cikin watan Ramadan.

Sarkin, ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, jim kaɗan bayan ya jagoranci dubun-dubatar al’umma sallar Idi a filin Idi na Ƙofar Mata da ke birnin Kano.

A cikin huɗubarsa, Sanusi, ya bayyana cewa azumin watan Ramadan bai tsaya ga barin cin abinci da sha kaɗai ba; ya haɗa da koyar da darusan tausayi, haƙuri, da tallafa wa juna.

Ya kuma ƙarfafi Musulmi da su ci gaba da kula da marasa galihu, musamman marayu da gajiyayyu.

Haka kuma, Sarkin ya yi kiran a tsananta addu’o’in neman ɗorewar zaman lafiya da haɗin kai a Jihar Kano da ma Najeriya baki ɗaya, yana mai jaddada cewa zaman lafiya shi ne ƙashin bayan kowane irin ci gaba.

Sarkin ya ƙara da yin addu’ar samun zaman lafiya a duniya da kuma roƙon Allah Ya kawo damina mai albarka, domin manoma su samu amfanin gona mai yawa.

Daga ƙarshe, ya shawarci iyaye da su jajirce wajen lura da tarbiyyar yaransu, inda ya bayyana cewa ingantacciyar tarbiyya ita ce ginshiƙin gina al’umma ta gari.

Manyan jami’an gwamnati, ciki har da Gwamnan Jihar Kano, suna daga cikin sahun farko na waɗanda suka halarci sallar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *