Rawar Da Sashen Ayyukan Hidimomi Da Biyan Bukatu Ke Kara Takawa A Kasar Sin
[ad_1]
Ci gaban tattalin arziki yana kunshe ne da muhimman abubuwa guda biyu, na farko kasuwancin kayayyaki, na biyu kuma kasuwancin ayyukan kwadago ko gudanar da hidima ko kashe kudi don biyan wata bukata (ma’ana, kamar ka ziyarci wani wuri da ba zai yiwu ka shiga ko ka yi amfani da kayan wurin ba sai ka biya kudi irin su: cibiyoyin wasanni da na nishadi da sauransu). A dukkan wadannan sassan biyu, kasar Sin ta nace ga gudanar da gyare-gyare don habaka su a turbarta ta zamanantarwa.
A kwanan baya, kasar ta fitar da wani tsari da zai gaggauta samar da sabbin ginshikai da za su karfafa samun ci gaba wajen kara yawan kashe kudade a bangaren hidimomi da kuma biyan bukatu. Dama dai tun a ’yan shekarun da suka gabata, tsarin ingiza sayayya ya sauya daga mayar da hankali ga bangaren sayayyar kayayyaki kawai, zuwa karfafa gudunmawar da bangaren ayyukan hidimomi da biyan bukatu zai bayar ga ci gaban tattalin arziki. A halin yanzu, za a iya cewa kwalliya tana biyan kudin sabulu domin an samu karin kason kudaden da al’ummar kasar Sin ke kashewa a bangaren hidimomi da biyan bukatu, inda hakan ya mayar da sashen a matsayin daya daga cikin sabbin ginshikan samar da ci gaban tattalin arziki mai inganci.
Daga shekarar 2020 zuwa 2025, kiyasin kudaden da kowane mutum yake kashewa a bangaren hidimomi da biyan bukatu ya karu da matsakaicin ma’auni da kaso 8.5 a cikin dari a bisa mizanin shekara-shekara. Haka nan a 2025, kudaden da aka kashe a bangaren sayayya da gudanar da hidimomi da biyan bukatu a bisa kiyasin kowane mutum sun karu da kaso 46.1, inda kuma har ila yau aka samu karuwarsu da kaso 3.5 a cikin dari a mizanin shekara-shekara.
Bari na ba da misali da gudunmawar da bangaren biyan bukatu ke bayarwa. A tsakanin 1 ga watan Nuwambar 2025 zuwa 31 ga Janairun 2026, adadin ziyarar da aka kawo cibiyoyin wasannin kankara a fadin kasar Sin ya kai miliyan 118, ciki har da adadin ziyarar bakin da suka zo daga waje da ya kai miliyan 1 da dubu 255.
Kazalika, kudin da aka samu a tsakanin wannan lokaci a cibiyoyin wasannin kankara da harabobinsu ya kai RMB yuan biliyan 69.15. Wannan fa a bangare guda ke nan, wanda bai kunshi lissafin na bangaren wasannin gaba daya ba, da gidajen cin abinci, da na kallon sinima, da hayar ababen hawa, da sauran cibiyoyin harkokin rayuwa. Wannan yana daya daga cikin siffofin katafariyar kasuwar kasar Sin wacce take ci gaba da samun sabbin dabaru masu habaka ci gabanta da kuma karfafa juriyar tattalin arzikin kasar, duk kuwa da yanayi na rashin tabbas da ake fama da shi a fagen kasa da kasa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link