Amfani Da Wayewar Kai Shi Ne Mafi Dacewa Wajen Samar Da Zaman Lafiya A Duniya
[ad_1]
Idan aka yi magana kan wayewa, wani lamari ne da ya jibanci ci gaban al’umma ta fannin al’adu, shugabanci, fasaha, birane, da kuma tsarin zamantakewar al’umma.
Bisa ga la’akari da yadda al’amurra a duniya suke cikin halin rudani da rashin tabbas, gami da yadda ake samun sauye-sauyen lamurra a cikin sauri a duniya, ya sanya shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya kaddamar da wata shawara ta inganta wayewar kai a duniya a matsayin wani yunkurin diplomasiyya da nufin samar da wata dama ta musayar al’adu tsakanin al’ummomi maimakon nuna kyama ko raini tsakanin al’umma, koyon darasi daga juna maimakon fito na fito da juna, da kuma rayuwar lumana da zaman lafiya maimakon nuna girman kai, gadara ko fifiko.
A kwanakin baya, CGTN da jami’ar Renmin ta kasar Sin suka hada gwiwa suka gudanar da bincike kan ra’ayin jama’a game da muhimmancin wannan shawara ta yin amfani da wayewar kai wajen samar da daidaito cikin lamurran duniya. An kuwa gudanar da wannan bincike ne a kan mutane 12,302 daga kasashe daban daban har 41 na duniya, inda daukacin mutanen suka yabawa wannan shawara ta inganta wayewar kai a duniya, inda suka yi amanar cewa, muhimman ginshikan wannan yunkuri da suka hada da mutunta al’adu da wayewar kan al’ummomi daban daban, assasa mutunci da kimar bil adam suna da matukar muhimmanci a wannan yanayi da duniya take ciki a halin yanzu.
Binciken ya nuna cewa, kashi 90.8 na mutanen sun yi amannar cewa, mutunta mabambantan al’adu na al’ummomi shi ne muhimmin tafarki da ya kamata a ce duniya tana kai. Kashi 77.2 kuwa suna da ra’ayin cewa babu wata al’umma da za ta dauki wayewarta a matsayin wadda ta fi ta sauran al’ummomin duniya. Yayin da kashi 93.1 na mutane daga nahiyar Afirka da kuma kashi 90.3 na mutanen yankin kudancin America suna da ra’ayi mai karfi ma cewa duk wayewa abu daya ne.
Kome ke nan dai, muhimmin abin da ya kamata mu lura a nan shi ne duniya na kunshe da mutane iri iri da suka sha bamban da juna, ya Allah ko ta launin fata, ko jinsi, ko harshe da dai makamantan hakan, kuma suka watsu a doron kasa, ya kuma zama wajibi a yi cudanya da juna. Domin samun kyakkyawar cudanya tsakanin irin wadannan al’ummomi, ya zama wajibi a fahimci al’adu da wayewar kan juna domin samun kyakkyawar ma’amala tsakanin juna.
Wannan shawara ta inganta wayewar kai a duniya da Sin ta kaddamar shekaru uku da suka gabata ta kara jaddada muhimmancinta a halin da duniya take ciki yanzu. Wayewar kai shi ne abu mai muhimmanci da zai samar da zaman lafiya a duniya. Da a ce America tana amfani da wayewar kai da ba ta haddasa fitina ba a yankin gabas ta tsakiya, ko muzgunawa kasashen ta hanyar harajin cinikayya, ko ta kai hari kan wata kasa ta kama shugaban kasar ta kuma daure shi, abin da ya karya dokar kasa da kasa. Sabo da haka wayewar kai ita ce hanya mafi a’ala wajen samar da daidaiton al’amurra da zaman lafiya a duniya. Matukar babu irin wannan wayewar kai, to babu shakka rashin daidaiton lamurra, rashin hakuri, girman kai, nuna fifiko da gadara da kama karya za su yawaita a cikin al’umma. (Lawal Mamuda)
[ad_2]
Source link