Ba a ga jinjirin watan Shawwal a Najeriya ba — Sarkin Musulmi

[ad_1]



Majalisar Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, tare da haɗin gwiwar Kwamitin Ƙasa na Ganin Wata, sun sanar da cewa ba su samu rahoton ganin jinjirin watan Shawwal ba a ko ina a Najeriya.

Sakamakon haka, majalisar ta ayyana ranar Juma’a a matsayin 1 ga watan Shawwal na shekarar 1447 bayan hijira, wadda ta yi daidai da 20 ga watan Maris, 2026.

Hakan na nufin ranar Juma’a za ta kasance ita ce ranar ƙaramar sallar bana.

Haka kuma, Musulmi a faɗin Najeriya za su azumci ranar Alhamis domin cike azumin watan Ramadan zuwa 30, kasancewar ba a ga jinjirin watan Shawwal ba.

Sarkin Musulmi, ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumi, tare da yin kira gare su da su ci gaba da yin ibada da ayyukan alheri.

Ya ce: “A ci gaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya da aminci da kwanciyar hankali, da kuma neman sauƙin halin da ake ciki.”

Ya ƙara da cewa: “A riƙa yi wa shugabanni addu’a domin Allah Ya ɗora su a kan abin da zai zama maslaha da alheri ga wannan ƙasa.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *