Kashe Larijani ba zai taɓa tsarin siyasar Iran ba — Minista




Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi ya bayyana cewa kisan gillar da Amurka da Isra’ila ke yi ba zai taɓa “ƙwaƙƙwaran tsarin siyasar” Tehran ba.

Ministan ya bayyana cewa kisan da Isra’ila ta yi wa Ali Larijani, babban sakataren majalisar ƙoli ta tsaron ƙasa na Iran, ba zai zama babban rauni ga shugabancin ƙasar ba.

A wata tattaunawa da gidan talabijin na Al Jazeera ya yi da shi, wacce aka nuna bayan da Tehran ta tabbatar da mutuwar Larijani a safiyar ranar Laraba, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce har yanzu Amurka da Isra’ila ba su gane cewa gwamnatin Iran ba ta dogara da mutum guda ba.

“Ban san dalilin da ya sa har yanzu Amurkawa da Isra’ilawa ba su fahimci wannan gaɓar ba: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da ƙwaƙƙwaran tsarin siyasa tare da kafuwar hukumomin siyasa, tattalin arziki, da na zamantakewa,” in ji Araghchi.

Ya ƙara da cewa, “Kasancewa ko rashin mutum guda ba ya shafar wannan tsari.

Tabbas, ɗaiɗaikun mutane suna da tasiri, kuma kowane mutum yana taka tasa rawar – wasu sun fi wasu, wasu kuma ƙasa da hakan – amma abin da ke da muhimmanci shi ne tsarin siyasar Iran tsari ne mai matuƙar ƙarfi.”

Araghchi ya kafa misali da kisan jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, wanda aka kashe a ranar farko na harin Amurka da Isra’ila a ranar 28 ga Fabrairu, inda ya lura cewa duk da gagarumin rashi da ƙasar ta yi, “tsarin ya ci gaba da tafiya.”

“Ba mu taɓa samun wanda ya kai jagoran ƙasar muhimmanci ba, kuma ko da shi ɗin ma ya yi shahada, tsarin ya ci gaba da aikinsa kuma nan take aka samar da wanda zai maye gurbinsa,” in ji Ministan.

Ya ƙara da cewa, “Idan wani daban ya yi shahada, haka ne zai faru. Idan har Ministan Harkokin Wajen ma ya yi shahada, tabbas za a samu wani wanda zai maye gurbinsa.”




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *