Gwamnonin Arewa Sun Yi Allah-wadai Da Hare-haren Ƙunar Baƙin Wake A Maiduguri

[ad_1]

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi Allah-wadai da mummunan fashewar bama-bamai da ta girgiza Maiduguri a yammacin ranar Litinin, yana mai bayyana harin a matsayin barazana ga al’ummomin yankin.

Rahotanni sun ce fashe-fashen sun faru kusan a lokaci guda a ƙofar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, zagayen Kasuwar Litinin da kuma yankin Ofishin Wasiƙa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

  • Zulum Ya Yi Allah-Wadai Da Fashewar Bam A Maiduguri, Ya Buƙaci A Ƙara Tsaro A Wuraren Ibada
  • Ko Za A Ga Sauyi Bayan Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka?

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar a ranar Talata, Gwamna Yahaya ya nuna matuƙar alhini kan wannan mummunan lamari, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Jihar Borno, musamman iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

“Wannan mummunan lamari ba kawai abin ƙyama ba ne, har ila yau wata muguwar ƙoƙari ce ta jefa tsoro da kuma tarwatsa zaman lafiyar da ake ƙoƙarin dawo da shi a yankin Arewa maso Gabas. Hari ne ga ɗan’adam baki ɗaya, kuma dole ne a yi Allah-wadai da shi da kakkausar murya,” in ji gwamnan.

Shugaban NSGF ɗin ya kuma jajanta wa waɗanda suka samu raunuka ke karɓar magani a asibitoci daban-daban, yana addu’ar samun sauƙi cikin gaggawa gare su, tare da yaba wa masu aikin agaji na farko da jami’an tsaro bisa gaggawar da suka yi wajen shawo kan lamarin bayan fashe-fashen.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *