IRGC ta sha alwashin kashe Netanyahu yayin da yaƙin Iran ya tsananta
[ad_1]
Rundunar dakarun juyin juya hali ta Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) ta Iran ta yi barazanar kashe Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, yayin da yaƙi ya tsananta a Gabas ta Tsakiya.
Barazanar ta fito ne a wata sanarwa da rundunar ta fitar a safiyar Lahadi, inda ta ce za ta ci gaba da bibiyar Netanyahu har sai ta “ga bayansa” kafin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a yankin.
A daren Asabar zuwa safiyar Lahadi, Iran ta harba makamai masu linzami zuwa tsakiyar Isra’ila, lamarin da ya haddasa fashe-fashe masu ƙarfi a Tel Aviv, kamar yadda wasu bidiyoyi da suka yaɗu a kafafen sada zumunta suka nuna.
Sai dai Isra’ila ta ce tsarin yi wa sararin samaniyarta garkuwa ya yi nasarar tare yawancin makaman da Iran ta harba, duk da cewa wasu rahotanni sun nuna an samu ɓarna a wasu sassan ƙasar.
Sabbin hare-haren na zuwa ne bayan Amurka ta kai farmaki a birnin Isfahan na Iran da kuma tsibirin Kharg, inda rahotanni suka ce mutum 16 da ke aiki a matatar mai suka mutu.
Tsibirin Kharg na ɗaya daga cikin muhimman wuraren da Iran ke fitar da man fetur, kuma ana kallonsa a matsayin muhimmin ginshiƙi ga tattalin arzikin ƙasar.
Iran ta yi iƙirarin cewa Amurkan ta yi amfani da sararin samaniyar Haɗɗdiyar Daular Larabawa wajen kai mata harin a Kharg, sai dai har kawo yanzu Washington da Abu Dhabi ba su ce komai game da zargin ba, yayin da aka ga yadda Tehran ta kai hari wasu sassa na Dubai a jiyan.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link