’Yan bindiga sun kashe mutum 20 a Filato

[ad_1]



Aƙalla mutum 20 ne suka mutu a wani hari da ’yan bindiga suka kai wani ƙauye a Jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya, kamar yadda wata ƙungiyar raya yankin ta bayyana.

Ƙungiyar Kanam Development Association (KADA) ta ce harin ya faru ne ranar Juma’a lokacin da maharan suka yi wa sojojin da ke sintiri a yankin kwanton ɓauna.

Sanarwar ta ce a yayin musayar wuta da ta biyo bayan harin, mutum 12 daga cikin jami’an tsaro sun rasa rayukansu, tare da wasu mutum takwas daga cikin mazauna yankin da suka haɗa kai da su domin kare al’ummarsu.

Kazalika, ’yan bindigar sun afka wa wata al’umma da ke kusa, inda suka kwashe dukiya ciki har da shanu.

KADA ta ce hare-haren sun ƙara jefa mazauna karkara cikin mawuyacin hali, domin a baya ma yankunan sun sha fama da hare-hare da sace-sacen mutane domin neman kuɗin fansa.

A Najeriya dai, ƙungiyoyin ’yan bindiga na yawan kai hare-hare a yankunan karkara, inda suke sace mutane da kwasar dukiya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *