Gabas Ta Tsakiya: Najeriya ta fara kwaso ’yan ƙasarta daga Iran ta iyakar Armenia

[ad_1]



Gwamnatin Tarayya ta fara kwashe wasu ’yan Najeriya da ke zaune a ƙasar Iran waɗanda suka buƙaci a dawo da su gida, sakamakon rikicin da ke ƙara ƙamari a yankin Gabas ta Tsakiya.

Jami’an ofishin jakadancin Najeriya sun raka wasu daga cikin ’yan Najeriya zuwa iyakar ƙasar Armenia domin su tsallaka zuwa waje mai tsaro.

Daraktan yaɗa labarai na Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM), Abdur-Rahman Balogun ne, ya bayyana hakan a ranar Laraba, yana mai cewa bayanin ya fito ne daga shugabar hukumar, Abike Dabiri-Erewa.

Ya ce: “Wasu ’yan Najeriya da suka nuna buƙatar su fice daga Iran domin tsira sun samu rakiyar jami’an ofishin jakadancin Najeriya har zuwa iyakar Armenia domin su tsallaka cikin aminci.”

Shugabar hukumar ta kuma bayyana cewa kawo yanzu babu wani ɗan Najeriya a Iran da rikicin ya shafa.

Ta ce jami’an gwamnati suna kan iyakar Iran da Armenia domin karɓar duk wanda ke son barin ƙasar.

Hukumomi sun ce suna aiki tare da ofisoshin jakadanci da sauran abokan hulɗa domin tabbatar da cewa an samar da tsaro da takardun tafiya ga duk ’yan Najeriya da ke son a kwaso su.

Dangane da jiragen da za su dawo da su gida, Dabiri-Erewa ta ce a halin yanzu sararin samaniyar yankin ba shi da tsaro saboda hare-haren da ke aukuwa.

Ta ƙara da cewa: “Da zarar an buɗe sararin samaniyar yankin, tawagar Gwamnatin Tarayya da ta ƙunshi jami’ai daga ma’aikatu daban-daban za su fara aikin kwaso ’yan Najeriya zuwa gida.”

Wannan mataki na zuwa ne yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara tsananta, lamarin da ya sa ƙasashe da dama suka fara kwashe ’yan ƙasarsu daga yankin.

An fara wannan rikicin ne kwanaki 12 da suka gabata bayan wani hari da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar a kan Iran, wanda ya haddasa sabon tashin hankali a yankin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *