’Yan bindiga sun kashe mutum 11 a Katsina

[ad_1]



’Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 11 tare da jikkata wasu da dama a wani hari da suka kai garin Dansoda da ke Ƙaramar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina.

Rahotanni sun ce harin ya faru ne ranar Litinin daddare, a daidai lokacin da al’umma da dama ke hutawa bayan buɗa baki a cikin wannan wata na Ramadan.

Lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin alhini da takaici, inda mazauna garin ke bayyana harin a matsayin babban zalunci ga mutane masu zaman lafiya.

Wani mazaunin yankin da ya tsallake rijiya da baya wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ’yan bindigar sun shiga garin ne da daddare suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

Ya ƙara da cewa, Ƙaramar Hukumar Kankara na daga cikin yankunan da a baya aka yi yarjejeniyar sulhu da ’yan bindigar, amma a cewarsa hakan bai hana su ci gaba da kawo hare-haren ba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga jami’an tsaro dangane da harin, duk da ƙoƙarin jin ta bakinsu da aka yi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *