Pakistan ta yi wa sabon jagoran Iran ta’aziyyar mahaifinsa

[ad_1]



Gwamnatin Pakistan ta taya sabon jagoran addinin Iran Mojtaba Khamenei murna kan naɗinsa a matsayin jagoran ƙasar, tare da miƙa ta’aziyya kan rasuwar mahaifinsa kuma tsohon jagora Ayatollah Ali Khamenei.

Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ne ya bayyana hakan a wata wasiƙa da ya aike wa Mojtaba Khamenei bayan hawansa kan kujerar jagoranci, a daidai lokacin da rikicin da ke tsakanin Iran da ƙawancen Amurka da Isra’ila ke ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya.

A cikin wasiƙar da ofishin firaministan ya fitar, Sharif ya bayyana “ta’aziyya da addu’o’in Pakistan” kan rasuwar Ali Khamenei, yana mai cewa mutuwarsa ta girgiza al’ummar Pakistan.

“Rasuwar Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ta yi matuƙar ba al’ummar Pakistan baƙin ciki, kuma muna tare da shugabanni da al’ummar Iran a wannan mawuyacin lokaci,” in ji shi.

Sharif ya kuma taya Mojtaba Khamenei murna kan ɗaukar ragamar jagorancin ƙasar, yana mai bayyana fatan cewa shugabancinsa zai jagoranci Iran zuwa zaman lafiya, kwanciyar hankali, mutunci da ci gaba a shekaru masu zuwa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *