Kotu Ta Ci Tarar Gwamnatin Kano Miliyan 1 A Shari’arta Da Tsofaffin Kwamishinoni

[ad_1]

Wata kotun ma’aikata da ke zamanta a Jihar Kano, ta umarci gwamnatin jihar ta biya tarar naira miliyan ɗaya a shari’ar da wasu tsofaffin kwamishinonin jihar suka shigar kan motocin gwamnati da aka ba su lokacin da suke riƙe da muƙami.

Kotun, wadda Mahmood Abba Namtari ke jagoranta, ta yanke hukuncin ne a ranar Talata bayan lauyan gwamnati ya nemi a ɗage shari’ar domin samun lokacin da zai shirya martaninsa.

  • Rikice-rikicen Da Suka Addabi PDP Ne Suka Sa Na Koma APC — Gwamnan Zamfara
  • Ramadan: ‘Yansanda Sun Buƙaci A Sanya Ido A Kano A Goman Ƙarshe

Lauyan gwamnati, Barista S. U. Jibril, ya shaida wa kotu cewa an sanar da shi batun shari’ar ne a ranar Litinin da rana, don haka bai samu isasshen lokaci ba don shirya takardun da ake buƙata.

Sai dai lauyan masu ƙara, Suraj Sa’ed (SAN), ya ce ba su da matsala kan ɗage shari’ar, amma ya roƙi kotu ta saka tarar kuɗi tun an riga an miƙa wa gwamnati takardun shari’ar.

Mai shari’a Namtari ya ce bayanai sun nuna an miƙa takardun tun a ranar 26 ga watan Fabrairu.

Daga nan kotun ta umarci a biya Naira 200,000 a kowace daga cikin shari’o’i biyar, wanda ya kai jimillar kuɗin zuwa Naira miliyan ɗaya.

Sannan ta ɗage shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Afrilu, 2026.

Tsofaffin kwamishinonin suna neman kotu ta hana gwamnatin jihar ƙwace motocin gwamnati da aka ba su lokacin da suke riƙe da muƙamansu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *