Yadda matasa suka yi aikin gayya don gyara hanyoyi a Kafanchan
[ad_1]
Matasa da dama a garin Kafanchan, da ke Ƙaramar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, sun yi aikin gayya domin gyara hanyar garin.
Sun yi amfani da gatari, fatanya, diga da sauran kayan aiki wajen yi wa hanyar gyara.
Aikin ya haɗa da haƙa da faɗaɗa magudanan ruwa don kaucewa ambaliya da kuma hana hanyar ƙara lalacewa.
Shugaban ƙungiyar Kafanchan Youth Forum, Injiniya Sa’adu Bako, ya ce sun yi aikin ne domin rage wahalar da jama’a ke sha, musamman wajen zuwa jana’iza, musamman a lokacin damina.
Ya kuma yi kira ga gwamnati ta gyara hanyar, kasancewar ba maƙabarta kaɗai take kai wa ba, har da ƙauyukan manoma kamar Zauru da Kurdan.
“Ina kira ga Gwamna Uba Sani ya saurari koke-kokenmu, domin gyaran hanyar don sauƙaƙa rayuwar jama’a kuma ya taimaka wajen harkar kasuwanci da fitar da amfanin gona,” in ji shi.
Ya gode wa matasan da suka fito aikin sa-kan da kuma mutanen da suka tallafa musu da kuɗi da kayan aiki.
Wasu mazauna yankin sun kuma roƙi gwamnati ta kula da hanyoyin cikin garin Kafanchan, kasancewar jama’ar yankin manoma ne da ke buƙatar hanyoyin mota don fitar da amfanin gonakinsu.
Go hotunan yadda matasan suka gudanar da aikin:
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link