Napoli ta samu nasara a gida karon farko tun watan Janairu
[ad_1]
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Napoli ta samu nasara a gida karon farko a gasar Serie A tun daga ƙarshen watan Janairu, bayan ta doke Torino da ci 2–1 a wasan da aka buga ranar Juma’a.
Zakarun gasar na bara sun yi wa Torino shigar wuri a fafatawar, inda Alisson Santos ya zura ƙwallo a minti na bakwai da fara wasa.
Daga bisani kuma Eljif Elmas ya ƙara ta biyu a minti na 68, kafin Cesare Casadei ya jefa ƙwallon da ta rage wa Torino rata ana daf da ƙarasa wasan.
Da wannan nasara, Napoli ta ƙara tabbatar da matsayinta a na uku a teburin gasar, lamarin da ke ba ta damar kusantar samun gurbin buga Gasar Zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.
Haka kuma ta rage tazarar makin da ke tsakaninta da ta biyu, AC Milan, zuwa maki guda kacal.
Sai dai AC Milan na da damar ƙara bai wa Napoli tazara idan ta samu nasara a wasan hamayya na Milan Derby da Inter Milan a ranar Lahadi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link