Karuwar Ma’aunin Tattalin Arzikin GDPn Kasar Sin Za Ta Zarce Yuan Triliyan 6 A Shekarar 2026
[ad_1]
Yau Jumma’a da yamma, agogon Beijing, an yi taron manema labarai game da zama na hudu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin wato NPC karo na 14 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda aka gayyaci manyan jami’an kasar Sin da suka hada da shugaban kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima Zheng Shanjie da dai sauransu, don su yi bayani game da batutuwan dake shafar tattalin arzikin kasar Sin.
A yayin taron, Zheng Shanjie ya bayyana cewa, hasashen da aka yi ya nuna cewa, a bana, karuwar ma’aunin tattalin arzikin GDPn kasar Sin zai zarce Yuan triliyan 6 a shekarar 2026. A sa’i daya kuma, za a zurfafa aikin raya fasahar AI, inda zuwa karshen shekarar 2030, jimillar darajar sana’o’i masu nasaba da fasahar AI za ta kai sama da triliyan 10. Ban da haka kuma, kwamitin zai hada kai da hukumomin da abin ya shafa, domin fitar da jerin matakai masu inganci, ta yadda za a habaka sana’o’in ba da hidima da darajarsu ta zarce triliyan 100 a tsakanin shekarar 2026 zuwa shekarar 2030, wato lokacin da za a aiwatar da daftarin shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arzikin kasa da zamantakewar al’umma karo na 15.
Mista Zheng ya kuma kara da cewa, sun yi imanin za a cimma burin raya tattalin arziki bisa karfin tattalin arzikin kasa, da yadda kasar ta kware a fannin yin kirkire-kirkire, da kuma kyawawan manufofinta. Haka zalika, kasar Sin tana da karfi da dabaru wajen fuskantar sauyawar yanayin kasuwanni, da kalubaloli, don haka tabbas, za ta cimma burin da ta tsara kamar yadda ake fatan gani. (Mai Fassara: Maryam Yang)
[ad_2]
Source link