Mutane 3 Da Za Su Iya Maye Gurbin Mataimakin Gwamnan Kano

[ad_1]

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, bisa zargin rashin ɗa’a mai tsanani, da cin zarafin ofis da kuma cin amana.

Jagoran masu rinjaye a majalisar, Lawan Hussaini Dala, ne ya gabatar da takardar tsige shi a zaman majalisar, yana mai cewa an ɗauki matakin ne bisa tanadin sashi na 188 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 da aka gyara.

  • Ba Zamu Lamunci Buƙatar Murabus Ɗin Mataimakin Gwamna Ba — Kwankwasiyya
  • Doguwa Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Kano

Dala ya zargi Gwarzo da hannu wajen karkatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomi lokacin da yake kwamishinan ƙananan hukumomi tsakanin 2023 da 2024, inda ya ce ana zargin yana karbar Naira miliyan 1.5 daga kowace ƙaramar hukuma 44 duk wata, abin da ya kai kusan Naira miliyan 462 cikin watanni bakwai.

Sai dai wasu masu sharhi kan siyasar Kano na ganin cewa rikicin siyasa ne ya jawo yunƙurin tsige shi, musamman bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, yayin da mataimakinsa ya ci gaba da kasancewa a jam’iyyar NNPP tare da jagoranta Rabiu Musa Kwankwaso.

Rahotanni sun ce idan an tsige Gwarzo, ana hasashen wasu ‘yan siyasa kamar Murtala Sule Garo, Salihu Sagir Takai ko kuma kakakin majalisar Jibril Ismail Falgore na iya maye gurbinsa a matsayin mataimakin gwamnan jihar.

Rahotanni sun nuna cewa ana ambaton wasu fitattun ‘yan siyasar da za su iya maye gurbin Gwarzo idan aka tsige shi. Cikinsu akwai tsohon ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2023, Murtala Sule Garo.

Haka kuma ana hasashen tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaben 2015, Salihu Sagir Takai, da kuma kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Ismail Falgore, na daga cikin waɗanda ake ganin za su iya maye gurbin mataimakin gwamnan idan aka kammala tsarin tsige shi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *