Sin Ta Yi Kira Da A Kauracewa Raba Kafa A Yaki Da Ta’addanci
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya ce wajibi ne kasashen duniya su yi watsi da salon zaben matakan da suka yi musu dadi kadai, su kuma kauracewa raba kafa yayin da ake yaki da ta’addanci, kana su kawar da duk wasu damammaki na kyankyashe ta’addanci, ta hanyar rage aukuwar tashe-tashen hankula, da talauci, da martaba cudanyar mabambantan wayewar kai.
Fu Cong, ya ce a halin da ake ciki, ta’addanci na kara cudanya da sauran laifuka masu nasaba da makamai, da manyan laifukan da ake aikatawa tsakanin kasashe, da rashin daidaito tsakanin al’umma, da amfani da sabbin fasahohin zamani ta hanyoyin da ba su dace ba. Ya ce wadannan kalubale masu sarkakiya sun haifar da mummunan tasiri ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.
Wakilin na Sin ya kuma ce gwamnatin kasar Sin na dora muhimmancin gaske ga aiwatar da dabarun dakile ta’addanci a matakin kasa da kasa, kuma tana taka rawar gani wajen ingiza hadin gwiwa tsakaninta da daidaikun kasashe da kasashe masu yawa, tana kuma goyon bayan ayyuka daban daban a nahiyar Afirka da tsakiyar Asiya, karkashin asusun samar da zaman lafiya da ci gaba na Sin da MDD.
Daga nan sai jami’in ya ce Sin a shirye take ta shiga a dama da ita, a aiki karo na tara na bitar dabaru, da hada karfi da dukkanin sassa wajen bayar da gagarumar gudummawar cimma burin wanzar da zaman lafiya da tsaron duniya na bai daya. (Saminu Alhassan)