Shugabannin Iraƙi sun yi alhinin mutuwar Khamenei

[ad_1]



Shugabanni da manyan jiga-jigan siyasar Iraƙi, ciki har da fitaccen malamin addini Moqtada al-Sadr, sun bayyana alhini da jimami kan mutuwar Jagoran Ƙoli na Iran, Ali Khamenei, wanda rahotanni suka ce ya rasu sakamakon wani gagarumin harin haɗin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai.

Wata haɗakar jagoranci da ta ƙunshi ƙungiyoyin Shi’a masu kusanci da Iran, Coordination Framework, ta ce, “cikin matuƙar alhini da baƙin ciki, muna jimamin rasuwar jagora shahidi, Ayatollah Ali Khamenei.”

Ƙungiyar ta ƙara da cewa, “jininsa zai ci gaba da zama haske abun jagora ga dukkan al’umma a zamunna masu zuwa,” tare da bayyana cewa “la’anta ta har abada za ta ci gaba da bin Yahudawa masu goyon bayan Isra’ila.”

A nasa ɓangaren, Moqtada al-Sadr a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa, “muna miƙa ta’aziyyarmu ga duniyar Musulunci,” tare da ayyana kwanaki uku na zaman makoki.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *