An ayyana dokar ta-ɓaci a Isra’ila kan fargabar martanin Iran
Isra’ila ta ayyana dokar ta-ɓaci ta musamman a faɗin ƙasar bayan sanar da ƙaddamar da wani sabon harin gargaɗi na haɗin gwiwa tare da Amurka kan Iran a ranar Asabar.
Cikin wata sanarwar gargaɗi da ya fitar, Ministan tsaron ƙasar, Israel Katz, ya bayyana cewa, Isra’ila ta kai harin ne a matsayin “hari na rigakafi” domin kawar da wata babbar barazana.
A yayin da tuni Iran ta soma mayar da martani, Isra’ila ta haramta tarukan jama’a tare da rufe duk makarantu da wuraren aiki, sannan ta mayar da majinyata da ke asibitoci zuwa wasu wurare a ƙarƙashin ƙasa.
’Yan sandan Isra’ila sun yi kira da jama’a da su jingine duk wasu tafiye-tafiye ba su zama tilas ba, domin bai wa motocin jami’an tsaro da na agajin gaggawa gudanar da zirga-zirga cikin sauƙi.
Amurka da Isra’ila sun kunna wutar da ba za su iya kashewa ba — Iran
Shugaban Kwamitin Tsaron Ƙasa na Majalisar Dokokin Iran, Ebrahim Azizi, ya ce harin da Isra’ila da Amurka suka kai mata tamkar sun kunno wutar da ba za su iya kashewa ba.
Azizi ya ce “mun gargaɗe ku! Amma kuka zaɓi kunno wutar da ba za ku iya kashewa ba” a wani saƙo da ya wallafa jim kaɗan bayan ƙaddamar masu da harin.
Iran ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya
Iran ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya game da hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai mata da safiyar yau.
Cikin wata sanarwa da rundunar sojin Isra’ila, IDF ta fitar, ta tabbatar da gano makamai masu linzami da Iran ta harba cikin Isra’ila, amma tana ƙoƙarin ganin ta kakkaɓo su.
Haka ma Qatar ta tabbatar da cewa Iran ta kai hari kan wasu sansanonin sojin Amurka da ke ƙasar, kodayake ta ce an kakkaɓo hare-haren.
Ita ma ƙasar Bahrain ta tabbatar da kai hari kan sansanonin sojin ruwan Amurka da ke ƙasar, kodayake ba ta alaƙanta harin da kowace ƙasa ba.
Amurka ta ce za ta ci gaba da hare-hare
Wani jami’in Amurka ya shaida wa Al Jazeera cewa ƙasar za ta ci gaba da kai manyan hare-hare ta sama da ta teku kan Iran.
Jami’in ya ce hare-haren na da nufin raunana tsarin tsaron Iran ne, kuma a halin yanzu an taƙaita su ne ga wurare a cikin Iran kaɗai.
Ya kuma tabbatar da cewa sojojin saman Amurka za su ci gaba da luguden wuta tare da haɗin gwiwa da rundunar sojin Isra’ila.
Ƙungiyar Iraƙi ta yi barazanar kai hare-hare kan sansanonin Amurka
Ƙungiyar mayaƙan Kataib Hezbollah da ke Iraƙi ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za ta soma kai hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka, a matsayin martani ga hare-haren da aka kai wa ƙungiyar.
Kataib Hezbollah na daga cikin manyan ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin Popular Mobilisation Forces (PMF), wadda aka kafa a 2014 domin daƙile hare-haren ISIL a wancan lokaci.
Rahotanni sun ce mayaƙa biyu sun rasa rayukansu a hare-haren sama da suka auka wa sansanin Jurf al-Sakher (Jurf al-Nasr) da ke Kudancin Iraƙi.
Ƙasashen duniya na ci gaba da mayar da martani
Ministan Harkokin Wajen Belgium, Maxime Prevot, ya ce bai dace a ɗora wa al’ummar Iran alhakin da ba nasu ba.
A cewar Ministan Harkokin Wajen Norway, Espen Barth, duk da yake Isra’ila ta bayyana harin a matsayin na rigakafi, sai dai bai dace da dokar ƙasa da ƙasa ba, yana mai cewa dole sai an samu wata barazana ta buƙatar gaggawa kafin a halatta irin wannan hari.
Shi ma Ministan Harkokin Wajen Pakistan, Ishaq Dar, ya yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai wa Iran wanda ya bayyana cewa babu wata hujja ta ƙaddamar da su. Ya yi kira da a dakatar da rikicin nan take ta hanyar dawo da tattaunawar diflomasiyya domin samun mafita cikin lumana.