Har Yanzu Nijeriya Tana Fatan Zuwa Kofin Duniya Na 2026
[ad_1]
Har yanzu ana zaman rashin tabbas, yayin da masoya ƙwallon ƙafa a Nijeriya ke jiran hukuncin da hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA za ta yanke kan ƙorafin da Nijeriya ta shigar kan zargin DR Congo da yin amfani da Ƴan wasan da ba su kamata ba a wasannin neman gurbin gasar cin kofin duniya ta 2026.
Tawagar Congo ta cire Nijeriya ne a bugun fenariti a watan Nuwamba domin samun gurbi a wasannin neman gurbi na duniya da za a buga. Amma kuma a cikin watan Disamba Nijeriya ta shigar da ƙorafi, inda ta zargin tawagar Congo da yin amfani da Ƴan wasa Aaron Wan-Bissaka da Aɗel Tuanzebe – waɗanda dukkanin su sun taɓa buga wa Ingila wasa a tawagar matasa, inda Nijeriya ta ce ba su cancanta ba domin dokar ƙasar Congo ba ta amince da Ƴanwasa da suke da takardar zama ɗan ƙasa na ƙasashe biyu ba
- Sharuɗan Da Chelle Ya Gindaya Wa NFF Domin Cigaba Da Jagorantar Super Eagles
- AFCON 2025: Dalilin Da Ya Sa Super Eagles Ba Ta Jira Bikin Karɓar Kyautar Tagulla Ba – NFF
Yayin da wani sashe na magoya bayan tawagar Nijeriya ke fatan ganin ƙasar ta samu wata damar, wasu kuma na ganin cewa tamkar babu adalci idan aka bai wa Nijeriya dama a kan DR Congo. FIFA ta tabbatar da cewa tana nazari kan ƙorafin, to amma ba ta sanar da ranar da za ta yi nazari ko kuma sanar da hukuncin da ta yanke ba, kuma tuni hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Nijeriya – NFF – ta musanta raɗe-raɗin cewa an yi watsi da ƙorafin nata.
Babban daraktan yaɗa labaran hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa Demola Olajire ya bayyana cewa duk wani batu da ke cewa an yanke hukunci ba gaskiya ba ne. Ya ƙara da cewa FIFA ba ta faɗa wa Nijeriya ko hukumar ƙwallon ƙafa ta Congo game da wani hukunci ba.
A lokacin da Nijeriya ta shigar da ƙorafi, shugaban NFF Mohammed Sanusi ya zargi DR Congo da karya dokokin FIFA.
Bayan wasannin neman gurbi, Tuanzebe da Wan-Bissaka sun kuma buga wa tawagar DR Congo a gasar cin kofin Afirka ta 2025 a Moroko. Amma kuma dokar ƙasar Congo ta ce ɗan wasa ba zai zamo mai takardar zama ɗan ƙasa biyu ba, amma wasu daga cikin Ƴan wasansu na da fasfo na ƙasashen Turai da kuma Faransa.
Tawagar Congo za ta kara da ko dai ƙasar New Caledonia ko Jamaica a karawar da za yi ta wasannin neman gurbi tsakanin ƙasashen duniya a watan Maris. Wanda ya yi nasara a wasan zai shiga cikin jerin ƙasashe 48 da za su buga gasar kofin duniya, a rukunin K, tare da ƙasashen Portugal da Uzbekistan da kuma Colombia.
Hukuncin Da Ake Sa Ran FIFA Za Ta Yanke
Kora: Idan FIFA ta yanke hukuncin cewa dalilan Nijeriya ba su da ƙarfi za ta iya watsi da ƙorafin, ta kuma ƙyale DR Congo ta ci gaba da wasan neman gurbin gasar cin kofin duniya.
Bincike da yin hukunci: FIFA za ta iya yin bincike game da ƙorafin, idan ta gano cewa akwai saɓa ƙa’ida wajen tantance Ƴan wasa, za ta hukunta hukumar (ta hanyar cin tara ko gargaɗi) ba tare da sauya sakamako ba.
Yin hukunci: Idan abin ya yi ƙamari, FIFA ko kuma Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka za su iya sokewa ko kuma ƙwace maki daga mai laifi a miƙa wa mai ƙorafi ko kuma a cire wa ƙasar maki daga cikin wasannin da aka yi na cikin rukuni. A baya, akan yi wannan hukunci ne idan aka gano ƙarara cewa an take doka, ko dai ta hanyar bayar da bayanan ƙarya ko kuma sauya wasu bayanai.
Duk da cewa Nijeriya ta lashe lambar tagulla a gasar cin kofin Afirka ta 2025, wanda ya sanya ta ƙara ɗabbaƙa kanta a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da suka gawurta a ɓangaren ƙwallon ƙafa a nahiyar, amma abin da ya fito fili shi ne, a halin yanzu, Nijeriya ba za ta je gasar cin kofin duniya ba, in dai ba wani abu ya sauya ba.
[ad_2]
Source link