Matar kwamandan Boko Haram ta miƙa wuya ga sojoji a Borno

[ad_1]



Wata mata da ake zargin ‘yar Boko Haram ce kuma matar ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar ta miƙa wuya ga sojojin Operation Hadin Kai a Konduga, Jihar Borno.

Majiyoyin soji sun ce matar, mai suna Kaltum Dalha mai shekaru 25, ta miƙa wuya a sansanin soji na Forward Operating Base da misalin ƙarfe 11:00 na safe ranar Laraba, 26 ga Fabrairu.

Rahotanni sun nuna cewa ta iso daga ƙauyen Sabsawa tare da ɗanta mai shekaru biyu.

Binciken farko ya nuna cewa mijinta, wanda aka ce shi ne kwamandan ‘yan ta’adda a yankin Mairam Buri, ya mutu ne a yayin wani artabu da sojoji suka yi da ‘yan Boko Haram kwanan nan.

Aminiya ta ruwaito cewa mutuwar mijin ne ta tilasta mata miƙa wuya, inda ta shaida wa jami’an tsaro cewa ƙungiyar ta fara wargajewa bayan kashe kwamandanta.

Sojojin Operation Hadin Kai sun ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare a ‘yan watannin nan, lamarin da ya kai ga kashe manyan ‘yan ta’adda, kama wasu a raye, ƙwato makamai da harsasai, da kuma miƙa wuya da mayaƙa da iyalansu da dama da suka yi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *