Jadawalin zagayen ’yan 16 na Gasar Zakarun Turai ta bana
[ad_1]
A Juma’ar da ta gabata ce Hukumar Ƙwallon Ƙafar Turai UEFA ta fitar da jadawalin zagayen ’yan 16 na Gasar Zakarun Turai ta wannan kaka.
Wannan na zuwa ne bayan kammala matakin neman gurbi da wasu ƙungiyoyi suka yi a tsakiyar mako bayan rashin samun damar tsallakawa zagayen ’yan 16 kai tsaye tun a matakin rukuni.
A jadawalin da UEFA ta fitar, an kammala haɗa ƙungiyoyin da za su kece raini a zagayen ’yan 16, inda mai kare kambi PSG za ta kara da Chelsea.
Sauran ƙungiyoyin da za su yi karon-batta da juna a sabon jadawalin sun hada da:
Galatasaray da Liverpool
Real Madrid da Manchester City
Atalanta a Bayern Munich
Newcastle United in Barcelona
Atletico Madrid a Tottenham
Bodo/Glimt a cikin Sporting CP
Bayer Leverkusen da Arsenal
Ƙiris ya rage ƙungiyoyin Italiya su yi abin kunya a gasar Champions League ta bana, inda ƙungiya daya ce ta samu damar tsallakawa wannan mataki, wato Atalanta wadda za ta kara da Bayern Munich ta Jamus.
Duk da cewa ƙungiyoyin Ingila shida ne suka kai matakin ’an 16, amma a cikinsu babu wadda za ta haɗu da ’yar uwarta.
Sauran wasannin da ake ganin za su yi zafi a gasar su ne karon-batta da za a sake yi tsakanin Real Madrid da Manchester City da kuma Newcastle da Barcelona.
Za a buga fallen farko na wasannin ne ranakun 10 da kuma 11 ga watan Maris, sannan a buga falle biyu na wasannin a ranakun 17 da 18 ga watan na Maris.
A ranar 30 ga watan Mayu ne za a buga wasan ƙarshe na gasar a filin wasa na Puskas Arena da ke birnin Budapest a ƙasar Hungary.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link