An Gudanar Da Taron Hukumar Harkokin Siyasa Ta Kwamitin Tsakiya Na JKS
An gudanar da taron hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin wato JKS a yau 27 ga wannan wata, inda aka tattauna kan daftarin shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15 na kasar Sin da rahoton aikin gwamnatin kasar da majalisar gudanarwar kasar take shirin mikawa taro na 4 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin na 14 domin yin bincike. Babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping ne ya shugabanci taron. Kuma yayin taron, an jaddada cewa, sa kaimi ga raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma a yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 zai biya bukatun zaman rayuwar jama’a, da raya sha’anin dan Adam a dukkan fannoni, da samun wadata tare, da kuma tabbatar da samun muhimmin ci gaba kan cimma burin zamanantar da kasa bisa tsarin gurguzu. (Zainab Zhang)