An lakaɗa wa matashi dukan da ya yi ajalinsa kan zargin fyaɗe a Bayelsa
[ad_1]
An lakaɗa wa wani matashi mai shekaru 38, Samuel Ofiri, dukan da ya yi ajalinsa kan zargin yi wa wata mata fyaɗe a yankin Otuoke da Karamar Hukumar Ogbia ta Jihar Bayelsa.
Bayanai sun ce wasu matasan unguwa ne suka yi wa mutumin duka tsiya sannan suka rufe shi a wani ɗaki suka riƙa azabtar da shi har sai da ya ce ga garinku nan.
Wannan lamari dai kamar yadda Aminiya ta ruwaito, ya tayar da hankalin mazauna yankin, musamman ɗalibai na Jami’ar Tarayya ta Otuoke.
Tuni dai mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar, DSP Musa Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an kama mutane biyar da ake zargi da hannu a lamarin.
A cewarsa, ana tsare da ababen zargin Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.
Mai magana da yawun rundunar ya ambato Kwamishinan ’Yan sandan jihar yana gargaɗin jama’a da su guji ɗaukar doka a hannu, inda ya yi kira da a riƙa kai rahoton duk wani abu da ake zargi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link