Jami’in Kasar Sin: Zargin Da Kasar Amurka Ta Yi Ba Shi Da Tushe


Jakadan kasar Sin mai kula da batun kwance damarar soja, Shen Jian, ya yi bayani kan matsayar kasar Sin dangane da shirin rage makamai da tabbatar da tsaro a duniya, wajen wani zaman mako-mako na taron yin shawarwari kan batun kwance damara, wanda ya gudana a birnin Geneva na kasar Switzerland a jiya Litinin.

A cewar jami’in na kasar Sin, shirin rage makaman nukiliya na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali a duniya, musamman ma ta fuskar manyan tsare-tsare. Saboda haka, kamata ya yi, gamayyar kasa da kasa su tsaya kan manufar nuna adalci da sanin-ya-kamata, yayin da ake aiwatar da matakan kayyade makaman nukiliya, da nacewa ga yunkurin hana bazuwar makaman nukiliya ta hanyar siyasa da ta diflomasiyya, da bin dokokin kasa da kasa, da kokarin farfado da tsarin kwance damarar soja da ya shafi bangarorin duniya daban daban.

Shen Jian ya kuma jaddada cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan yarjejeniyar hana yin gwajin makaman nukiliya. Kana zargin da kasar Amurka ta yi wa kasar Sin, cewa wai ta kaddamar da gwajin makaman nukiliya, sam ba shi da tushe. Wanda ya nuna niyyar kasar Amurka ta fakewa da lamarin don sake kaddamar da gwaje-gwajen makaman nukiliya a cikin gidanta. Saboda haka, kasar Sin ta kalubalanci bangaren Amurka da ya sake bayyana goyon bayansa ga alkawarin da kasashe 5 masu makaman nukiliya suka dauka na dakatar da dukkan gwaje-gwajen makaman nukiliya, gami da aiwatar da matsayar da bangarorin duniya suka cimma a wannan fanni. (Bello Wang)



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *