Ana zaman ɗar-ɗar bayan kashe madugun dillalan ƙwayoyi a Mexico

[ad_1]



An shiga zaman ɗar-ɗar bayan sojojin Mexico sun sanar da kashe ƙasurgumin madugun fataucin miyagun ƙwayoyi, Nemesio Oseguera Cervantes, wanda aka fi sani da El Mencho.

Oseguera, wanda Fadar White House take zarginsa da shigo da miyagun ƙwayoyi ciki har da fentanyl zuwa Amurka, ya yi gamo da ƙarshensa ne a yayin wani samame da ya haddasa tashin hankali a sassa daban-daban na ƙasar Mexico.

A wata sanarwa da rundunar sojin ƙasar ta fitar, Oseguera mai shekaru 59, wanda shi ne jagoran ƙungiyar dillalan miyagun ƙwayoyi ta Jalisco New Generation, ya jikkata ne a artabu da sojoji a garin Tapalpa na Jihar Jalisco, inda daga bisani ya rasu yayin da ake jigilar sa zuwa Mexico City.

Bayan samamen, wasu ’yan ƙungiyoyi dillalan miyagun ƙwayoyi masu ɗauke da bindigogi suka mayar da martani ta hanyar toshe manyan hanyoyi sama da 20 a yammacin Jalisco, tare da ƙona motoci.

Rikicin ya bazu zuwa jihohi da dama, lamarin da ya sa aƙalla jihohi takwas suka dakatar da karatun makarantu kai-tsaye, yayin da ɓangaren shari’a ya ba alƙali damar rufe kotuna idan buƙatar hakan ta taso.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito Shugabar Mexico, Claudia Sheinbaum, tana kira ga ‘yan ƙasa da su kwantar da hankalinsu.

A cewar sojojin, an kashe wasu mutane shida da ake zargi ‘yan ƙungiyar ne, yayin da sojoji uku suka jikkata.

Kazalika, an kama mutane biyu tare da ƙwato makamai iri-iri, ciki har da na’urar harba roka.

AFP ya ce an soke dukkan tarukan jama’a a Jihar Jalisco, wadda ke shirin karɓar baƙuncin wasannin Gasar Kofin Duniya ta bana.

Titunan Guadalajara sun yi shiru yayin da shaguna da gidajen mai suka rufe.

Amurka, wadda hukumar tsaronta ba daɗewa ta sanya tukwicin dala miliyan 15 kan duk wanda ya taimaka aka kama Oseguera, ta tabbatar da bayar da bayanan leƙen asiri a samamen, inda Fadar White House ta bayyana lamarin a matsayin gagarumar nasara.

Haka kuma, Guatemala ta ce ta ƙara tsaro a kan iyakarta da Mexico sakamakon barazanar ƙungiyoyin masu laifi.

Ƙungiyar Jalisco New Generation, wadda aka kafa a 2009, na daga cikin mafi hatsari a Mexico, kuma tuni Amurka ta ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta’addanci.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *