Ning Zhongyan Ya Lashe Lambar Zinare A Tseren Gudun Kankara Na Mita 1,500 Na Maza A Gasar Olympics Ta Hunturu Ta Milan-Cortina
[ad_1]
Dan wasan motsa jiki na kasar Sin, Ning Zhongyan, ya yi wa Jordan Stolz na Amurka kancal inda ya lashe tseren gudun kankara na mita 1,500 na maza a gasar wasannin Olympics ta hunturu ta Milan da Cortina, a jiya Alhamis.
Ning, wanda ya lashe tagulla biyu a tseren mita 1,000 na maza da kuma tseren tawaga, ya kafa wani sabon tarihi a gasar Olympics na gudun minti daya da dakika 41.98, inda ya lashe wa kasar Sin lambar zinare ta farko a gasar Olympics a wannan wasan, kana lambar yabo ta uku a wasannin da ake yi.
Bayan nasarar da ya samu a tseren mita 1,000 da na 500, Stolz ya kammala a dakika 0.77 a bayan Ning inda ya samu lambar azurfa a tseren mita 1,500, yayin da kuma mai kare kambunsa a gasar ta Olympics Kjeld Nuis na kasar Netherlands ya samu lambar tagulla a gudun minti 1:42.82. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link