Jami’an Tsaro Sun Kashe Dan Ta’adda, Kachalla Kabiru A Jihar Kogi

[ad_1]

Jami’an Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Rundunar Sojin Kasa ta Nijeriya (Nigerian Army), da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (Department of State Services – DSS) sun kashe jagoran ‘yan bindiga, Kachalla Kabiru, tare da wasu manyan mataimakansa a wani samame na hadin gwiwa da aka kai a Jihar Kogi.

Majiyoyin tsaro masu inganci sun bayyana cewa an gudanar da wannan samame ne a ranar 13 ga Fabrairu, 2026, bayan makonni na tattara bayanan sirri da sa ido da suka tabbatar da kasancewar Kabiru a wani Boyayyen wuri da aka gano. Har ila yau, an yi amfani da hare-haren sama na musamman da Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (Nigerian Air Force) ta kai domin kai farmakin.

  • Samar Da Motoci Masu Sulke: Ministan Tsaro Ya Yaba Da Jajircewar Gwamnan Zamfara A Fannin Tsaro
  • Ramadan: Hisbah Ta Kama Mutane 9 Bisa Zargin Cin Abinci A Bainar Jama’a

A cewar majiyar, “An kashe Kachalla Kabiru da wasu manyan mataimakansa a wani kakkarfan samame da ya hada da hare-haren sama da na kasa. An kai harin ne bayan sahihan bayanan sirri sun tabbatar da kasancewarsa a wurin da aka sa a gaba.”

Majiyar ta kara da cewa Kabiru na taka muhimmiyar rawa wajen daukar ‘yan bindiga aiki, tsarawa da jagorantar zirga-zirgarsu a jihohi da dama na yankin Arewa ta Tsakiya da makwabtanta.

Ta kuma ce, “Kabiru ya bar yankin Arewa maso Yamma ya koma Kogi fiye da shekaru 10 da suka wuce, inda ya kafa sansani a cikin dazuka da al’ummomin kan iyaka. Daga nan ne yake jagorantar ayyukan garkuwa da mutane da ta’addanci a jihohin Kogi, Kwara, Benue, Enugu, Edo, Ekiti da Ondo. Ya kasance babban ginshiki da ke hada kungiyoyin masu aikata laifi a tsakanin jihohi.”

Majiyar ta kara da cewa kashe Kabiru babban koma baya ne ga tsararrun ayyukan ‘yan bindiga a yankin Arewa ta Tsakiya, kuma ana sa ran hakan zai kawo tangarda ga hadin gwiwar ayyukan masu laifi.

Jami’an tsaron Nijeriya na ganin cewa Kabiru ya taka rawa sosai wajen samar da kayan aiki da daukar ma’aikata ga kungiyoyin ‘yan bindiga, tare da saukaka zirga-zirgar mayaka, makamai da wadanda aka sace ta hanyoyin dazuka daga Arewa maso Yamma zuwa yankunan Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Yamma.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *