Direbobi Sun Koka Kan Dawowar Matsalar Tsaro Kan Babbar Hanyar Damaturu Zuwa Biu
[ad_1]
Direbobi sun bukaci gwamnatin tarayya da Gwamnatin Jihar Borno, da su sake gina hanyar Damaturu zuwa Biu mai tsawon kilomita 85, wadda ta hada kananan hukumomi biyar a jihohin Yobe da Borno.
Mazauna yankin, sun nuna rashin jin dadinsu kan rashin kyawun hanyar, inda suka ce hakan ya janyo tsawaita lokacin tafiye-tafiye tare da tsananta matsalar tsaro. Kazalika, sun yi kira ga hukumomin tarayya da na jihohi da su gaggauta gyara hanyar, domin saukaka zirga-zirgar ababen hawa.
- Indomie Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Raya Al’adu A Bikin Kamun Kifi Na Argungu Karo Na 61
- Bayan Shekaru 7, DSS Ta Sake Buɗe Binciken Ɓacewar Dadiyata
A cewar matafiya da direbobi, lokacin tafiya kan babbar hanyar ya karu matuka daga kimanin sa’o’i biyu zuwa sama da sa’o’i shida, wanda hakan ya haifar da karuwar amfani da man fetur da yawan fashewar ababen hawa da kuma kara fuskantar hare-hare da sace-sacen ‘yan Boko Haram.
Malam Bukar Mustapha, wani direban mota ya ce; masu ababen hawa, suna bin hanyar ne a kullum cikin fargabar sace su daga ’yan tada kayar baya da ke cin gajiyar rashin kyawun hanyar.
Daily trust ta rawaito cewa, sojoji na bincikar hanyar kowace safiya, domin gano ababen fashewa da ake zargi kafin su bar masu ababen hawa su tafi.
Wata fasinja mai suna Fatima Modu ta shaida wa Daily trust cewa, wasu ‘yan bindiga ne suka sace ‘yan’uwanta a kan hanya makwanni biyu da suka wuce.
“Duk da kasancewar wuraren bincike na jami’an tsaro, amma har yanzu akwai matsala, domin kuwa ana ci gaba da samun asarar rayuka da dama, mata masu juna biyu da ke tafiya asibitoci don haihuwa ko kula da lafiyarsu na fuskantar kalubale sosai,” in ji ta.
Wani direban mota, Yusha’u Umar ya ce; rashin kyawun titin na jawo wa direbobi asara mai dimbin yawa, sakamakon gyare-gyaren ababen hawansu, kamar fashewar tayoyi da sauran matsalolin inji.
“A da, muna shafe sa’o’i biyu kacal daga Damaturu zuwa Biu, amma yanzu muna kwashe sama da sa’o’i shida, lamarin ya aara ta’azzara matsalar rashin tsaro, saboda ‘yan tada kayar baya suna amfani da munanan hanyoyin wajen kai hare-hare,” in ji shi.
Shugaban kungiyar NURTW, reshen Damaturu, Mohammed Maina, ya bayyana hanyar a matsayin wata “mummunan hanya” don haka, ya bukaci gwamnati ta sake gina ta, domin kare afkuwar hadura da hare-hare kan masu ababen hawa.
Duk kokarin jin ta bakin babban kwamandan ayyuka na gwamnatin tarayya a Jihar Yobe, amma abin ya ci tura, sakamakon an ce ba ya jihar, ya je wani aiki da aka tura shi.
[ad_2]
Source link