2027: Atiku Ya Gargaɗi Magoya Bayansa Kan Tsangwamar Jama’ar Peter Obi
[ad_1]
Tsohon mataimakin shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ya duƙufa wajen kwantar da tarzomar da ta kunno kai a tsakanin gamayyar jam’iyyar adawa, bayan takun saƙa a tsakanin magoya bayansa da magoya bayan Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, kan tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a 2027.
Wannan shiga tsakani, ya biyo bayan zazzafar muhawarar da aka shafe makwanni ana yi, musamman ta hanyar shafin X (Twitter), tun bayan da Obi ya sauya sheƙa daga jam’iyyar LP zuwa ADC a watan Disamba, matakin da ya ce; ya duƙufa wajen gina wata kafa ta ‘yan adawa mai ƙarfi da za ta iya tinkarar ƙalubalen tattalin arziƙin Nijeriya tare kuma da kawar da jam’iyyar APC mai mulki.
Tun bayan lokacin da Obi ya tsunduma cikin jam’iyyar, magoya bayansa, musamman ƴan ƙungiyar ‘Obidient Movement’, suka ƙara yin kira ga Atiku da ya goyi bayan takarar Obin na neman tikitin takarar shugaban ƙasa na ADC.
- Atiku Ne Ya Fi Dacewa Da Tikitin Takara A ADC Amma Ya Kamata Ya Janye — Baba-Ahmed
- Tsaro: Gwamnatin Nijeriya Ta Ɗauki Rayukan Mutane Da Muhimmanci – Peter Obi
Sai dai, matsin lamba ya haifar da koma baya daga magoya bayan Atiku, inda ya ƙara dagula rarrabuwar kawuna a tsakanin jam’iyyar tare da ƙara nuna damuwa kan haɗin kan cikin gida kafin 2027.
A ranar Talata, Atiku ya fito fili ya nemi a dakatar da hayaniyar, yana mai gargaɗin cewa; hare-haren da ake kai wa, ko dai kansa ko kan Obi na raunana ƴan adawa, wanda ko shakka babu akwai hannun APC a ciki.
A cikin wani rubutu a shafinsa na X, tsohon mataimakin shugaban ƙasar, ya buƙaci magoya bayansa, da su dakatar da abin da ya bayyana a matsayin “yaƙin basasa” mai cin gashin kansa a cikin ƙawancen.
“Duk wanda ya zagi Obi ko Atiku, ba ya neman shugabanni da gamayyar ADC da Nijeriya samun da nasara, waɗanda kawai ke cin gajiyar irin wannan yaƙin basasar su ne, ƴan ta’addar APC na birane da ke son ci gaba da riƙe matsayin shaiɗan, don haka yana da matuƙar kyau ya zama muna tare!” kamar yadda Atikun ya rubuta.
[ad_2]
Source link