Za a gudanar da wasannin ƙwallon yashi a Abuja

[ad_1]



Hukumar shirya gasar ƙwallon yashi ta ƙasa ta tabbatar da cewa za a gudanar da wasannin ƙarshe na bana a filin wasa na Jabi Lake Park, da ke babban birnin tarayya Abuja.

Kodinetan hukumar a Najeriya, kuma shugaban hukumar a nahiyar Afirka, Mahmud Hadejia, ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da Trust Radio a cikin shirin “Bakin Raga” da safiyar yau Laraba.

Shugaban ya bayyana cewa wannan ce gasa ta biyar da za a buga, kuma ta farko da za a fafata a Abuja.

A cewarsa, za a fara buga wasannin ƙarshe daga gobe Alhamis, 6 ga watan Nuwamba, sannan a kammala a ranar Lahadi, 9 ga watan Nuwamba, 2025.

Wannan dai gasa ce da kungiyoyin da suka fi fice a zagayen farko za su fafata a cikinta, wanda ya haɗa da jihoyin Akwa Ibom, Jigawa, Kebbi, Kaduna da wasu sauran jihohi.

Haka kuma, manyan baki da ake sa ran halartar bikin buɗe gasar a ranar Laraba, 5 ga watan Nuwamba, sun haɗa da Ahmed Musa, Ibrahim Musa Gusau, Seyi Tinubu, da sauran fitattun ‘yan wasa da jami’ai.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *