Yunƙurin Hana Gawuna Bin Kwankwasiyya, “An Neme Shi A Waya An Rasa”
[ad_1]
Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023, Nasir Yusuf Gawuna, yanzu ya zama ɗaya daga cikin ‘yan siyasar da ake nema ruwa a jallo a Kano, yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci wasu manyan jagororin jam’iyyar da su dakatar da shirinsa na sauya sheƙa zuwa tafiyar Kwankwasiyya, daga bisani zuwa jam’iyyar ADC.
Shirin Gawuna na haɗa kai da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin kayar da Gwamna Abba Kabir Yusuf a zaɓen 2027 na ƙara samun karɓuwa a Kano.
- Kotu Ta Ƙi Amincewa Da Buƙatar Dakatar Da Shirin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano
- Kasar Sin Ta Bayar Da Kyautar Sabon Rukunin Kayayyakin Kiwon Lafiya Ga Madagascar
Wannan mataki, ya fara haifar da ruɗani a cikin APC, inda ɓangaren Kwankwasiyya kuma ke cike da farin ciki kan wannan shirin sauya sheƙar.
Majiyoyi daga cikin jam’iyyar APC sun shaida wa jaridar Daily Nigeria cewa, a ‘yan kwanakin nan, ba a iya samun Gawuna a wayar salularsa, lamarin da ya ƙara janyo hasashe cewa yana ci gaba da tattaunawar siyasa a wajen ƙasar. Duk ƙoƙarin da manyan masu ruwa da tsaki a APC suka yi don tuntuɓarsa ya cutura.
Majiyoyi sun bayyana cewa Gawuna ya tafi ƙasar Saudiyya a watan Ramadan domin gudanar da Umrah, amma har yanzu bai dawo Nijeriya ba. Wata majiya mai masaniya kan motsinsa ta ce daga bisani tsohon mataimakin gwamnan ya wuce wata ƙasa a Arewacin Afirka domin hutun sirri.
A cewar majiyar, Gawuna ya sanya wayarsa a tsarin yadda kira ba zai shigo wayarsa ba, domin kauce wa matsin lamba da kuma yawan kiran waya daga shugabannin jam’iyyar da ke ƙoƙarin hana shi sauya sheƙa.
[ad_2]
Source link