Yaƙin Gabas Ta Tsakiya: Masu Tafiya Umrah Daga Nijeriya Na Fuskantar Cikas

[ad_1]

Akwai wani yanayi na rashin tabbas a tsakanin kamfanoni masu zaman kansu da kuma matafiya Umara daga Nijeriya zuwa ƙasar Saudiyya, yayin da yaƙin Iran da Amurka ke ci gaba da yin illa ga ayyukan jiragen sama da sauran harkokin kasuwanci.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, ɗimbin al’ummar musulmi suna zuwa ƙasar Saudiyya a cikin watan Ramadan, domin aikin Umara, inda sama da masu ibada miliyan 122 suka ziyarci ƙasar a cikin watan Ramadana na shekarar 2025.

  • WSCIJ Ta Naɗa Farfesa Umaru Pate A Kwamitin Amintattu
  • Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka

Sai dai kuma, tashin hankalin da ake fama da shi a Gabas ta Tsakiya, tare da rufe muhimman hanyoyin jiragen sama, irin su Doha da Dubai, na tilastawa maniyyata daga Nijeriya sake duba shirin tafiyar.

Tashe-tashen hankula sun ƙara zama abubuwan lura a kan tsaro da amincin jirgin da kuma zuwa a kan lokaci, domin gudanar da ibada, lamarin da ya sa mutane da dama, ba su da tabbas a kan ko za su samu damar zuwa aikin nasu na Umara a bana.

Ƙasashen Iran da Iraƙi da Isra’ila da Syria da Kuwait da Ƙatar da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa, sun sanar da cewa; an rufe sararin samaniyarsu, bayan da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran hari, lamarin da ya kawo dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na farar hula a Gabas ta Tsakiya.

Fitattun kamfanonin jiragen sama da suka dakatar ayyukan, sun haɗa da kamfanin Emirates, Etihad, Ƙatar Airways, Air France, British Airways, Syria Air, Air India, Turkish Airlines, EgyptAir, Lufthansa da kuma Habasha Airlines.

Sai dai, sauran kamfanonin jiragen saman irin su Saudi Arabian Airlines, na ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama zuwa ƙasar, saboda Saudiyya ba ta rufe sararin samaniyarta a hukumance ba, duk da katsewar yankin.

Sararin samaniyar Saudiyya na ci gaba da karɓar jiragen farar hula, bayan hare-haren ramuwar gayya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Duk da cewa dai kuma, hare-haren makami mai linzami da jiragen sama na baya-bayan nan da aka kai kan ababen more rayuwa na yankin Gulf, ciki har da harin da aka kai a wata cibiyar matatar mai a Saudiyya, ya haifar da fargabar cewa; Riyadh na iya sanya takunkumin sararin samaniya, idan rikicin ya ƙara tsananta.

Mahajjata suna bayyana ra’ayoyinsu kusan iri ɗaya, waɗanda suka zanta da Daily trust, sun bayyana ra’ayoyinsu daban-daban, inda wasu ke tunanin soke tafiye-tafiyen nasu.

Alhaji Auwal Sani, wanda ya yi niyyar zuwa aikin Umara a Kano, ya ce; an dakatar da tafiyasa wadda ya shirya yi a ranar Litinin.

“Zan yi tafi ne a jirgin Ƙatar Airways, amma sai na samu saƙo daga wurinsu cewa; an buɗe tikitin bayan an soke shi, haka kuma ba a ba ni bizar ba har yanzu, kuma na shirya tafiya tare da iyalina a yau, amma ga mu duk a maƙale, Allah ne mafi sanin abin da ya fi dacewa da mu.

“Sun ce za a buɗe sararin samaniya a ranar 6 ga watan Maris, sannan kuma za a ba mu biza, domin mu tafi,” in ji shi.

Salihu Shu’aibu, wanda ke shirin tafiya Umrah, ya ce; halin da ake ciki a halin yanzu ya sa shi cikin damuwa ƙwarai da gaske.

“Gaskiya, abin da yake faruwa, yana ba ni tsoro shi yasa nake tunanin ko kawai ma na soke tafiyar tawa kwata-kwata,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, tsoron abin da ba a sani ba, ya dabaibaye maniyyata da dama a Jihar Kwara.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *