Yadda jirage suka taƙaita ratsa Mashigar Hormuz

[ad_1]



Rahotanni sun nuna cewa jiragen ruwa na kasuwanci guda tara kacal ne aka gano sun ratsa ta Mashigar Hormuz tun daga ranar Litinin, sakamakon rikicin da ke ƙara tsananta a Gabas ta Tsakiya.

Bayanan da kamfanin sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa MarineTraffic ya tattara, wanda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya nazarta, sun nuna cewa daga cikin jiragen akwai tankokin mai, jiragen dakon kaya da kuma jiragen dakon kwantena.

Muhimmancin Mashigar Hormuz

Mashigar Hormuz na daga cikin manyan hanyoyin safarar makamashi a duniya, domin kusan kashi 20 cikin 100 na ɗanyen mai na duniya da kuma kusan irin wannan kaso na gas mai ruwa (LNG) na ratsa wannan mashiga.

A kowane lokaci akwai ɗaruruwan manyan jiragen ruwan dakon mai da aka faka su a Tekun Fasha, suna jiran wucewa ta wata hanya tsukakkiya wadda ƙaramin jirgin ruwa mai gudu zai iya wucewa a ƙasa da awa ɗaya.

Duk da haka, ta wannan hanya mai nisan kilomita 33, ake jigilar ɗanyen mai daga Saudiyya, Iraki, Kuwait da UAE a hankali, don ciyar da kasuwannin makamashi daga Tokyo zuwa Rotterdam.

Wannan hanya, wadda aka fi sani da Strait of Hormuz wato Mashigin Hormuz, a mafi yawan ƙididdiga ita ce hanyar ruwa mafi muhimmanci a fannin tattalin arzikin duniya.

Sai dai rikicin da ya barke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran ya sa yawancin jiragen ruwa suka dakatar da zirga-zirga a yankin.

Fargabar kai wa jirage hari

Rahotanni sun ce bayan kai hare-hare kan jirage uku a ranar Lahadi, wasu jiragen kaɗan ne suka kuskura suka ratsa mashigar, ciki har da tankokin mai uku da kuma jirgin dakon gas guda.

Wasu daga cikin jiragen sun rika ɓuya domin ratsa mashigar cikin sanɗa ta hanyar kashe na’urar AIS (Automatic Identification System), wadda ke nuna inda jirgi yake a teku.

Wani mai nazari a kamfanin Kpler, Matt Wright, ya ce duk da rikicin, har yanzu ana samun wasu jirage da ke zirga-zirga ta mashigar, amma da dama na yin hakan ne ba tare da kunna na’urorin sa ido ba.

Daga cikin jiragen da aka gano sun ratsa mashigar akwai: Kavomaleas, wani tankar mai da ya nuna sigina gabashin mashigar ranar 3 ga Maris kafin daga bisani ya sake nuna sigina cikin Tekun Gulf bayan awanni 14.

Haka kuma jirgin Athina ya nuna sigina a yammacin mashigar ranar 1 ga Maris bayan ya ɗauko mai a Bahrain, kafin daga bisani ya daina aika sigina.

Jaridar Financial Times ta ce aƙalla jirage biyar na kamfanin Dynacom sun ratsa mashigar tun bayan fara rikicin, duk da cewa sun kashe na’urorin gano motsinsu.

Masana sun ce yawaitar hare-hare kan jiragen ruwa na iya yin illa ga tattalin arzikin duniya, musamman idan aka yi la’akari da muhimmancin Mashigar Hormuz wajen jigilar makamashi.

Rundunar tsaron teku ta Birtaniya UK Maritime Trade Operations ta ce wani jirgi mai suna Safeen Prestige ya samu rauni bayan an harba masa makamai yayin da yake tafiya daga Tekun Gulf ranar Talata.

Sai dai kakakin rundunar sojin Iran, Abolfazl Shekarchi, ya ce Iran na tabbatar da tsaron mashigar, amma ba ta da niyyar rufe ta gaba ɗaya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *