Uwargidan Tinubu Ta Nemi A Ceto Ɗaliban Kebbi Cikin Ƙoshin Lafiya

[ad_1]


Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta nuna baƙin cikinta kan sace ɗalibai 25 na Makarantar Sakandare ta ’yan mata da ke Maga a Jihar Kebbi, da kuma kashe mataimakiyar shugaban makarantar.

A jawabin da ta fitar a ranar Talata, ta ce an ci zarafin yara marasa laifi, malamai masu jajircewa, da kuma tsaron da ya kamata makarantu su samar.

Ta ce Shugaba Bola Tinubu ya umarci jami’an tsaro su gaggauta ceto ɗaliban da kuma kama waɗanda suka aikata laifin.

Uwargidan Shugaban Ƙasa ta miƙa jajenta ga iyayen ɗaliban, abokanan karatunsu, da al’ummar makarantar.

Ta yi addu’ar Allah Ya dawo da ɗaliban lafiya, tare da addu’ar Allah Ya gafarta wa mataimakiyar shugabar makarantar da aka kashe.

Ta kuma buƙaci ’yan Nijeriya su kasance masu lura da goyon bayan ƙoƙarin jami’an tsaro, tana jaddada cewa kare yara ya zama babban abin da ƙasa ta fi mayar da hankali a kai.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *