Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan PDP A Sakkwato Ya Fice Daga Jam’iyyar

[ad_1]

Saidu Umar, tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato a zaɓen 2023, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.

Umar, wanda aka fi sani da Ubandoma Sakkwato ya bayyana hakan cikin wata wasiƙa mai ɗauke da ranar 10 ga watan Maris, 2026, wadda ya aike wa shugaban PDP na mazaɓar Sarkin Adar Kofar Atiku da ke ƙaramar hukumar Sakkwato ta Kudu.

  • Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 23
  • Majalisar NPC Ta Gudanar Da Zaman Rufe Taronta Na Shekara-shekara Na Bana

Matakin nasa na zuwa ne kwana guda bayan tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya fice daga jam’iyyar.

Umar ya ce ya bar PDP ne saboda rikice-rikicen cikin gida da kuma shari’o’in da ke gudana kan shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa, wanda ya ce sun raunana haɗin kan jam’iyyar.

Ya kuma gode wa jam’iyyar PDP bisa damar da ta ba shi ya tsaya takarar gwamna a zaɓen 2023, tare da yaba wa goyon bayan da ya samu daga shugabanni da mambobin jam’iyyar.

Umar ya ce duk da barinsa jam’iyyar, har yanzu yana da ƙudirin ci gaba da inganta shugabanci na gari da dimokuraɗiyya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *